Ya Kamata Ku Sani: Manyan Abubuwa 6 Masu Muhimmanci da Za Su Faru a Disambar 2024

Ya Kamata Ku Sani: Manyan Abubuwa 6 Masu Muhimmanci da Za Su Faru a Disambar 2024

A yayin da muka shigo cikin watan Disamba, akwai muhimman abubuwan da ya kamata 'yan Najeriya su kula da su, daga bukukuwan al'adu zuwa muhimman ranaku.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A cikin wannan rahoton, za mu haska manyan bukukuwa shida da za sun faru a Disamba, waɗanda ke shafar Najeriya da ma duniya baki daya.

Muhimman bukukuwa 6 da za a gudanar a watan Disambar 2024
Kirsimeti, ranar dambe da wasu muhimman bukukuwa 4 da za a gudanar a Disambar 2024. Hoto: Insta_kenya, Jacob Wackerhausen
Asali: Getty Images

Wadannan abubuwan su na ba al'umma damar sada zumunci, baiwa juna kyaututtuka, ziyartar wuraren shakatawa da kuma uwa uba samun hutu daga wajen aiki.

Ga jerin manyan abubuwa hudu masu muhimmanci da za su faru a watan karshe na shekarar 2024:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ranar cutar kanjamau ta duniya

Ana gudanar da bikin ranar cutar kanjamau (AIDS) ta duniya a ranar 1 ga watan Disambar kowacce shekara domin wayar da kan jama'a game da HIV/AIDS.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara cire haraji daga masu amfani da Opay, Moniepoint da sauran bankuna

Ana amfani da ranar ne domin wayar da kan jama'a kan yadda za su gujewa kamuwa da cutar, jinyar cutar da kuma ba da tallafi da karfafa guiwar masu dauke da ita.

Taken ranar AIDS ta duniya ta wannan shekarar shi ne: "Ka ɗauki hanyar da ta dace: Lafiyata, haƙƙina!" kamar yadda rahoton WHO (kungiyar lafiya ta duniya) ya nuna.

Kungiyoyi daban-daban, ciki har da NACA da UNAIDS, suna shirin gudanar da taron gwaje-gwaje kyauta da wayar da kai a cikin al'umma domin karfafa kokarin hana kamuwa da HIV.

2. Ranar bikin Kirsimetin 2024

Al'ummar Kirista na gudanar da bikin ranar Kirsimati domin tunawa da haihuwar Yesu Almasihu a ranar 25 ga Disamba a kalandar Gregorian, inji rahoton Britannica.

Bukukuwan Kirsimeti suna farawa daga farkon Disamba, tare da kawata gidaje, saka waƙoƙin yabo wanda ke kara karsashin bukin a cikin gidaje, coci, da wuraren jama'a.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Ranakun Hutu Da Yan Najeriya Za Su Mora A Disamba 2024/Janairu 2025

Al'ummomi suna shirya tarukan taimako, suna raba abinci, kaya da kyaututtuka ga waɗanda ba su da lafiya ko marasa galihu, sannan suna ƙarfafa saƙon soyayya a tsakaninsu.

Ana gudanar da tarukan addini musamman wa'azin ranar Kirsimeti, sannan ana gabatar da tsofaffin al'adu da na zamani a Najeriya da kasashen duniya.

3. Bikin ranar dambe ta duniya

Bikin ranar dambe al'adance da ake yi a Burtaniya da wasu kasashen Commonwealth, ciki har da Najeriya a ranar 26 ga watan Disamba.

Ranar dambe ta kasance ranar ba da kyaututtuka ce ga mabukata, wadda ta rikide zuwa wani bangare na bukukuwan Kirsimeti a cewar makalar WikiPedia.

A kasashe da dama, ranar dambe lokaci ne na taron iyali, wasannin motsa jiki da siyayya yayin da 'yan kasuwa ke sayar da kayansu a farashi mai rahusa.

Harkokin wasanni, musamman wasannin ƙwallon ƙafa da gasar doki, suna da muhimmanci a cikin murnar ranar dambe a kasashe da dama.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: An gano abin da zai iya hana NLC shiga yajin aiki a Disamba

4. Ranar sabuwar shekara

Ana bikin murnar sabuwar shekara a ranar 31 ga Disamba. Rana ce da ke nuna zuwan karshen shekarar da ake ciki.

Maza da mata, manya da yara kan taru a wurare daban daban domin gudanar da bikin, tun daga safiya har zuwa karfe 12:59 na ranar.

Idan dare ya yi, akan kunna wutar itace, yayin da manyan gine-gine kan sanya kayan kwalliya da agogo na kirga lokaci. Ana fara kirga lokaci idan ya rage dakiku 10 a shiga sabuwar shekara.

Birane a duk duniya, daga Times Square na New York zuwa Harbour na Sydney, suna shirya manyan murnar bukukuwa ta hanyar harba wuta mai fashewa a sararin samaniya.

5. Ranar Sambisa (Borno)

Ranar tunawa da Sambisa rana ce ta ranar hutu a jihar Borno Najeriya, wanda ke gudana a ranar 22 ga watan Disamba na kowace shekara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Babagana Zulum ne ya ware ranar domin tunawa da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu Bayan Tinubu Ya Kore Ta

Hakazalika, ana amfani da damar wajen murnar nasarorin da sojojin Najeriya suka samu da kuma tunawa da sojoji da 'yan sa kan da suka mutu wajen yakar Boko Haram.

6. Gasar wasan kwallon doki (Abuja)

Gasar kwallon doki (Polo) ta Abuja GPC 2024 za ta gudana daga ranar 4 zuwa 15 ga Disamba, 2024 a filin wasanni na Asokoro.

Taron zai ƙunshi wasanni masu ban sha'awa, yawon bude ido a cikin Aso Rock da ba da kyautuka kamar kyautar Guards Challenge da gasar cin kofin shugaban ƙasa.

Duba bayanin wasan a nan kasa:

Hutun da ma'aikata za su samu a Disamba

Tun da fari, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya musamman ma'aikata za su samu hutu hudu a tsakanin Disambar 2024 da Janairun 2025.

Ana sa ran gwamnatin tarayyar Najeriya za ta ayyana ranar Laraba, 25 ga Disamba, 2024, a matsayin ranar hutu na Kirsimeti, da dai sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.