Kasashe 5 da aka hana bikin Kirsimeti

Kasashe 5 da aka hana bikin Kirsimeti

A ranar 25 ga watan Disamba na kowacce shekara, mabiya addinin Kirista a Najeriya da sauran sassan duniya ke yin bikin murnar Kirsimeti domin nuna murna da farincikinsu da zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa.

Kiristoci a Najeriya kan dinka sabbin tufafin da zasu saka ranar Kirsimeti, sannan idan ranar ta zo su kan dafa abinci tare da ziyartar 'yan uwa da abokai da kuma gudanar da bukukuwa masu nishadantar wa da kayatar wa.

Sai dai, duk da wannan biki da ake yi a Najeriya da sauran kasashe a fadin duniya, akwai wasu kasashe da suka haramta bikin Kirsimeti.

Ga wasu kasashe biyar da yanzu haka ba a bikin Kirsimeti a cikinsu;

1. Somalia

Somalia kasa ce a yankin gabashin nahiyar Afrika da ta shafe fiye da shekaru 10 tana fama da yaki. Akwai mutane fiye da miliyan goma sha biyar a kasar kuma kaso 99.8% nasu Musulmai ne mabiya mazhabar Sunni.

A shekarar 2015 ne gwamnatin kasar Somalia ta haramta gudanar da bikin Kirsimeti.

BBC ta rawaito cewa babban jami'in gwamnatin kasar Somalia mai kula da harkokin shari'a da addini, Mohammed Kheyro, ya bayyana cewa, "ba daidai bane Musulmi a Somalia su yi bikin Kirsimeti, yin hakan haramun ne".

2. Brunei

Ana yi wa kasar Brunei kirari da 'gidan zaman lafiya', kasa ce dake kan wani tsuburi a kudu maso gabashin nahiyar Asia. Akwai mutane kusan 500,000 a kasar Brunei, kuma kusan 75% dinsu Musulmai ne.

Duk da Brunei tana da mabiya addinin Kirista da na Bhudda masu yawa, kasar tana bin tsarin addinin Islama ne.

Sultan Hassanal Bolkiah, shugaban Brunei, ya haramta bikin Kirsimeti a kasar a shekarar 2014 bayan kaddamar da tsarin shari'ar Musulunci. Doka ta tanadi hukucin cin tarar $20,000 ko kuma daurin shekaru biyar a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin yin bikin Kirsimeti a kasar, kamar yadda jaridar 'The Independent' ta kasar Ingila ta rawaito.

3. Koriya ta arewa

Koriya ta Arewa kasa ce a gefe guda a nahiyar Asia dake da yawan jama'ar da ya kai miliyan ashirin da biyar. Tun bayan kafuwar kasar a shekarar 1945, gidan wanda ya kafa ta, Kim II-sung, ne ke mulkinta.

Gwamnatin kasar Koriya ta Arewa bata rungumi wani addini a matsayin nata ba. Bincike ya nuna cewa a kalla kaso 64.3% na mutanen kasar basa wani addini, kaso 16% mabiya addinin 'Shamanism' na kasar ne , kaso 13.5% suna bin addinin 'Chondoism', kaso 4.5% mabiya addinin Bhudda, sai kuma Kirsitoci masu kaso 1.7%.

Babbu 'yancin yin addini a Koriya ta Arewa, lamarin da yasa gwamnatin kasar ta haramta dukkan wani bikin addini tun a shekarar 1948.

4. Saudi Arabia

Kasar Saudiyya ta haramta duk wani addini a kasarta idan ba Musulunci ba, lamarin da yasa jama'a basu yi mamaki ba don mahukuntan kasar sun haramta bikin Kirsimeti.

Akwai sabanin fahimta a tsakanin Musulmi da Kiristoci a kan Annabi Isa, wanda bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne mabiya addinin Kirista suke kira da Kirsimeti.

5. Tajikistan

Tajikistan kasa ce maras yalwar kasa a yankin tsakiyar nahiyar Asia dake da yawan mutane a kalla miliyan tara, kuma kaso 96% daga cikinsu mabiya addinin Musulunci ne, mazhabar Sunni.

A shekarar 2015 ne kasar Tajikistan ta haramta gudanar da duk wani nau'in biki da sunan Kirsimeti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng