Zulum Ya Kaddamar da Katafariyar Tashar Jirgin Kasa ta Farko a Arewa

Zulum Ya Kaddamar da Katafariyar Tashar Jirgin Kasa ta Farko a Arewa

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya fara aikin layin dogo na cikin gari domin haɗa Maiduguri da kewaye wanda shi ne na farko a Arewa
  • A matakin farko, aikin zai haɗa tasha 12 da ke cikin Maiduguri, inda za a haɗa kasuwanni, makarantu, wuraren da sauran wuraren hada hada
  • An bayyana cewa layin dogon zai sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki tare da ƙarfafa tattalin arziki da fadada kasuwanci a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum ya fara kokarin kafa tarihi wajen samar da jirgin kasa na zamani a Borno.

Kwamishinan sufuri da makamashi na jihar Borno ya bayyana cewa ana gudanar da bincike da shawarwari domin tabbatar da nasarar aikin.

Zulum
Za a samar da tasahr jirgin kasa a Maiduguri. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa kwamishinan ya ce aikin zai sauƙaƙa zirga-zirga tare da bunkasa kasuwancin mazauna Maiduguri.

Kara karanta wannan

Zulum ya fadi dalilin gwamnonin Arewa na son dakatar da kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gina titin jirgin kasar farko a Arewa

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar aikin samar da jirgin kasa na cikin gari wanda zai haɗa Maiduguri da kewaye.

Aikin da aka kaddamar tare da hadin gwiwar kamfanin EEC zai samar da tsarin sufuri na zamani wanda zai haɗa manyan wurare da ake hada hadar tattali a Maiduguri.

A matakin farko, za a gina tasha 12, ciki har da wuraren kasuwanci, makarantu, da wuraren ayyukan yau da kullum.

Amfanin da za a samu daga titin jirgin Maiduguri

Aikin layin dogon na cikin gari zai kawo sauƙi ga zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki, tare da rage kudin sufuri.

National Accord ta wallafa cewa tsarin sufuri zai bayar da sabuwar dama ga mazauna Maiduguri wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin sauƙi.

Titin jirgin kasa zai farfado da Borno

Kara karanta wannan

"Mutane sun zama mabarata," Jigon APC ya koka kan tsadar kayan abinci a Najeriya

Gwamna Zulum ya ce aikin titin jirgin kasan yana cikin shirinsa na farfado da zaman lafiya da tattalin arziki tare da sake fasalin gine-gine a jihar Borno.

Farfesa Zulum ya ce hakan ya zama dole sakamakon mummunar barnar da Boko Haram suka janyo tsawon shekaru da suka gabata.

Layin dogon Kano-Legas ya fara aiki

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa layin dogo da aka gina daga Legas zuwa Kano ya fara aikin jigilar kayayyaki.

Hakan ya fito fili ne a yayin wata ziyara da ministan sufuri, Saidu Alkali ya kai zuwa jihar Kano domin duba cigaban aikin layin dogon.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng