Za'a yi layin Dogo na jirgin kasa daga Kano ya shiga har kasar Nijar
- Ana kokarin karade kasar nan da titin jirgin kasa
- Ministan sufuri yace za'a kai layin har Maradi
- Nan gaba ma har Chadi za'a kai shi
Ministan sufuri na Najeriya, Mista Rotimi Amaechi, yace Najeriya na duba yiwuwar biyar da jiragen kasa da titunan su kasashen ketare, Nijar da Chadi, domin inganta harkokin sufuri da kyautata kasuwanci da dangantaka tsakanin kasashen Afirka.
A zantawarsa da manema labaria, Amechi, yace yanzu haka gwamnatin Tarayya na tattaunawa da shuwagabannin Nijar domin iyar da layin dogo da zai tashi daga Kanoyabi ta Jigawa, ya shiga Kazaure, Daura, Jibiya, ya isa har Maradi a kasar Nijar.
DUBA WANNAN: Dakwalen kaji da Najeriya ta samar wa duniya ta hanyar kimiyya
An kuma jiyo shi yana cewa akwai yiwuwar za'a kai layin dogon har Chadi, ta ratsa ta arewa maso gabashin kasar nan.
Akwai manyan ayyuka dai da gwamnatin Tarayya ke son yi, sai dai babu alamar zata iya cimmasu ganin lokaci ya qure saura wata takwas gwamnatin ta kare.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng