'Yan Sanda Sun Gwabza da 'Yan Bindiga da Tsakar Dare, An Raunata Miyagu
- Sufeto Janar na 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya yabawa jami'ai bisa tarin nasarorin da suka samu kan yan ta'adda a wasu jihohin Najeriya
- A Borno, jami'an 'yan sanda sun dakile hare-haren 'yan ta'adda a ofishin 'yan sandan Jakana, inda suka fatattaki maharan tare da raunata da dama
- A wasu jihohin Najeriya, jami'an 'yan sanda sun samu nasarar kakkabe sansanonin 'yan bindiga da kuma kwato makamai masu yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sufeto Janar na 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya jinjinawa jami'ai bisa jarumtar da suka nuna da kuma nasarorin da suka samu.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan sandan Najeriya suka yi artabu da miyagu wajen ceto rayuwar mutane a jihohi.
Kakakin Rundunar 'yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa a Facebook cewa za su ci gaba da kare rayukan 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun dakile 'yan ta'adda a Borno
Rundunar 'yan sanda da ke Borno ta yi nasarar hana wani harin wasu 'yan ta'adda a ranar 28 ga Nuwamba.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addar sun kai farmaki kan babban caji ofis din 'yan sanda a Jakana da misalin karfe 1 na dare.
Sai dai maharan sun gamu da matsananciyar turjiya daga jami'an 'yan sanda, wanda ya kai ga raunata da dama daga cikin su.
'Yan sanda sun kakkabe sansanin 'yan bindiga
A ranar 25 ga Nuwamba, 2024, jami'an 'yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami'an tsaro sun kai samame kan sansanonin 'yan bindiga a wurare daban-daban a jihar Sokoto.
A yayin farmakin, an samu nasarar kwato bindigogi AK-47 daya da tarin harsasai, yayin da 'yan bindigar suka tsere da gudu zuwa cikin daji.
An hana yunkurin satar mutane a Delta
A jihar Delta, jami'an 'yan sanda sun hana wani yunkurin satar mutane a ranar 28 ga Nuwamban 2024.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda sun bi bayan masu laifin tare da gwabzawa da su, inda suka tilasta musu tserewa daji.
Vanguard ta wallafa cewa an samu nasarar kwato bindiga AK-47 guda uku, wasu bindigogi guda biyu da tarin harsasai.
'Yan bindiga sun ta da bom a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa bam din da ‘yan bindiga suka dasa a kan wata gada a Maru ya yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Lahadi, 1 ga Disamba.
Rahoto ya ce 'yan bindigar sun kai harin ne domin ramuwar gayya bayan kashe jagoran ‘yan bindiga, Sani Black, a watan Satumba da ya gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng