Kudirin Haraji: Tambawul Ya bi Sahun Masu Sukar Tinubu, Ya Fadi Kuskuren da Ya Yi

Kudirin Haraji: Tambawul Ya bi Sahun Masu Sukar Tinubu, Ya Fadi Kuskuren da Ya Yi

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya fito ya nuna adawarsa da ƙudirin haraji da Bola Tinubu ya ɓullo da shi
  • Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya bayyana cewa sam ba yanzu ba ne lokacin da ya dace na fito da ƙudirin ba
  • Ya nuna cewa kamata ya yi gwamnati ta maida hankali wajen rage wahala ga ƴan Najeriya maimakon ƙara ɗora musu wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya soki ƙudirin haraji da shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

Tambawul ya bayyana cewa ba yanzu ba ne lokacin da ya kamata a fito da ƙudirin, duba da irin ƙalubalen tattalin arzikin da ƴan Najeriya ke fama da shi.

Tambuwal ya soki kudirin haraji
Tambuwal ya caccaki kudirin haraji na Tinubu Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tambuwal ya bayyana ra'ayinsa ne a ranar Lahadi, yayin da yake raba kayan agaji ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a mazaɓarsa ta sanata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Zulum ya fadi dalilin gwamnonin Arewa na son dakatar da kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma raba kayan fara sana'a ga sama da mutane 1,000 da suka ci gajiyar shirin koyon sana'o'i.

Abin da Tambuwal ya ce kan ƙudirin haraji

"Bari na yi amfani da wannan damar wajen yin magana kan abin da ya kunno kai a yanzu, batun sake fasalin haraji wanda Shugaba Bola Tinubu ya gabatar."
"Na yi imanin cewan wannan ba lokacin da ya dace ba ne na sake duba tsarin VAT ko kowane nau'i na haraji, lokacin bai yi ba, sam bai da ce ba."
"Wannan lokaci ne mai wahala ga al’ummar Najeriya da halin da suka tsinci kansu a ciki."
"Abin da muke bukata daga gwamnati shi ne ta maida hankali kan ayyuka da shirye-shiryen da za su kawo sauƙi ga jama’a ba wai ta ƙara musu wahala ba."
"Dama muna fama da tsadar rayuwa sakamakon karya darajar Naira da cire tallafin mai da wannan gwamnatin ta yi."
"Ina ganin kamata ya yi mu maida hankali wajen rage wahalar, tare da duba hanyoyin da za mu tsamo mutane daga cikin halin ƙunci."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi amfanin da cire tallafin man fetur ya yi wa Najeriya

- Aminu Waziri Tambuwal

Zuwa yanzu dai kudirin harajin dai ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawan Najeriya.

Ndume ya damu kan ƙudirin haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya nuna damuwa kan kuɗirin dokar sake fasalin haraji.

Sanata Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda takwarorinsa a majalisar dattawa suka amince da dokar sake fasalin haraji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng