An Tabbatar da Nadin na Kusa da Ganduje kuma Jigon APC a Matsayin Jagaban Musulmai

An Tabbatar da Nadin na Kusa da Ganduje kuma Jigon APC a Matsayin Jagaban Musulmai

  • Gamayyar limamai da malaman Musulunci sun amince da nadin sakataren APC ta kasa a matsayin Jagaban Musulmai
  • Limaman da malaman Musulunci sun amince tare da tabbatar da Surajudeen Ajibola Basiru a sarautar da ke wakiltar jihar Osun
  • Nadin na zuwa ne kwana ɗaya kafin Basiru ya halarci taron bude masallaci da Gidauniyar Ganduje ta gina tare da amininsa shugaban APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Sakataren jam'iyyar APC mai mulki, Surajudeen Ajibola Basiru ya samu babban mukami a jihar Osun.

Gamayyar malaman Musulunci da limamai sun tabbatar da Basiru a matsayin Jagaban Musulmai a jihar Osun.

Abokin Ganduje ya zama Jagaban Musulmai a Osun
An nada sakataren APC, Ajibola Basiru a matsayin Jagaban Musulmai a Osun. Hoto: Dr. Ajibola Basiru, Salihu Tanko Yakasai.
Asali: Facebook

Basiru, Ganduje sun halarci bude masallacin Juma'a

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata Basiru ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu zai wuce Afrika ta Kudu daga Faransa, an fadi lokacin da zai dawo Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndin na zuwa ne kwana ɗaya kafin Sanata Basiru ya raka abokinsa, shugaban APC, Abdullahi Ganduje zuwa jihar Kano.

Tsohon gwamnan Kano da Sanata Basiru sun ziyarci jihar domin bude masallacin Juma'a da makarantar Islamiyya da Gidauniyar Ganduje ta gina.

Basiru da manyan malaman Musulunci da suka hada da Sheikh Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe da kuma Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun sanya albarka kan wannan hidima.

Sanata Basiru ya zama Jagaban Musulman Osun

Dr. Basiru ya nuna jin dadinsa kan nadin sarautar da aka yi masa bayan amincewar malaman da limamai.

"Jagaban Musulmai na jihar Osun."
"Gamayyar limamai da malaman Musulunci a Osun sun amince da nadi na da kuma tabbatar da ni a matsayin Jagaban Musulmai a jihar."

- Dr. Ajibola Basiru

Sanata Basiru ya magantu kan rigima da Gwamna

A baya, kun ji cewa a ranar Laraba 28 ga watanYunin 2023 aka samu hatsaniya tsakanin gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da tsohon Sanata, Ajibola Basiru.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje da Aminu Ado sun bude masallacin Juma'a, an Musuluntar da mutane

Hakan ya samo asali ne kan wurin zama a masallacin Idin, yayin da aka buƙaci sanatan ya tashi ya ba gwamnan wuri don ya zauna.

Sanatan ya shawarci gwamnan da ka da ya bari wasu da ba 'yan cikin gwamnatinsa ba su ɓata masa tafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.