Sojojin Najeriya Sun Kwato Makamai, Sun Tarwatsa Sansanonin Ƴan Bindiga a Arewa

Sojojin Najeriya Sun Kwato Makamai, Sun Tarwatsa Sansanonin Ƴan Bindiga a Arewa

  • Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da farmakin tsaro a Taraba don hana ‘yan bindiga samun mafaka a garuruwan jihar
  • An rahoto cewa sojojin sun kakkabe 'yan ta'addar yankunan da ke kusa da Lijem, Vingiri, Kufai Ahmadu, Jam, Hingir da sauransu
  • An rusa sansanonin ‘yan bindiga, an kwato harsasai, babura, da rediyo, yayin da aka bukaci al’umma su ci gaba da ba da bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Rundunar Sojin Najeriya ta 6 Brigade, karkashin jagorancin Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ta tsananta hare hare a a Jihar Taraba.

An ce sojojin sun dage da kai farmaki kan sansanonin 'yan ta'adda a jihar domin ba al'umma kariya lokacin girbi da bukukuwan karshen shekara.

Sojojin Najeriya sun kakkabe sansanonin 'yan ta'adda a jihar Taraba
Sojojin Najeriya sun tsananta hare-hare a Taraba, an kakkabe sansanonin 'yan ta'adda. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Sojoji sun kakkabe 'yan ta'addar Lejem

Zagazola Makamala ya wallafa a X cewa, sojoji na kai farmakin ne domin hana ‘yan ta’adda samun mafaka a jihar tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sun kashe kwamandan ƴan ta'adda da wasu mutum 4 a Yobe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon shirin kai farmakin ya fara ne a ranar 28 ga Nuwamba 2024 a karamar hukumar Takum, inda aka durarwa maboyar ‘yan bindiga a yankin Lijem High Ground.

Sojojin sun mamaye yankin Lijem tare da fadada hare harensu kan 'yan bindigar yankin kauyukan Vingiri da Vingir, wanda ya dawo da kwanciyar hankali ga mazauna yankin.

Sojoji sun yi arangama da 'yan ta'adda

A ranakun 29 da 30 ga Nuwamba 2024, an kara gudanar da farmaki a kauyukan Kufai Ahmadu, Jam, Hingir, Ukum, da Nbaume, inda aka kai hari maboyar fitattun miyagun.

Sojojin sun gamu da ‘yan bindiga a sansanonin New Gboko da Che Adekpe, wadanda ke da alaka da fitaccen dan ta’adda Liamdoo Douglas Adekpe.

Zagazola Makama ya bayyana cewa 'yan ta'adar da aka fi sani da Boujogh, sun gwabza yaki da sojojin Najeriya a cikin kwanakin.

Taraba: Sojoji sun kwato makamai, babura

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa muka cafke 'dan jarida mai binciken kwa kwaf': Sojoji sun wanke kansu

Sojojin sun yi nasarar tarwatsa ‘yan bindigar tare da rusa sansanonin su. Haka kuma, an kwato harsasai 27, gidan harsashin AK-47 guda 1, rediyon Baofeng guda 1 da babura 2.

Don kara tabbatar da tsaro, sojojin sun ci gaba da sintiri a yankunan Akume da Ananum a karamar hukumar Donga, wanda ke nuna kishin su na kare rayuka a Taraba baki daya.

Birgediya Janar Uwa ya yabawa al’ummomin yankin bisa goyon bayansu, tare da bukatar su kasance masu lura da bayar da bayanai cikin lokaci ga hukumomin tsaro.

Taraba: Sojoji sun gano gidan hada makamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin Najeriya ta cafke wasu mutane a jihar Taraba da ake zargin suna hada kai da yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar soji a jihar Taraba, Kyaftin Oni Olubo ya tabbatar da cafke mutanen da ake zargin a ƙaramar hukumar Lau inda ya ce an kwato makamai masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.