'Kasuwancin Nono da Nama': Yadda Kasar Waje Ta Shirya Taimakawa Gwamnatin Kebbi

'Kasuwancin Nono da Nama': Yadda Kasar Waje Ta Shirya Taimakawa Gwamnatin Kebbi

  • Gwamnatin Indonesiya ta shirya tallafawa Najeriya don bunkasa samar da madara da nama a cikin shekaru biyar masu zuwa
  • Jakadan Indonesiya, Dakta Usra Harahap, ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kaiwa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi
  • Harahap ya ce hadin gwiwar zai taimaka wajen samar da kayan kiwo na zamani, tsarin kiwo mai dorewa, da karuwar ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Indonesiya ta bayyana shirinta na tallafawa Najeriya wajen bunkasa samar da madara da nama da kashi 60% da kuma 40% cikin shekaru biyar.

Jakadan Indonesiya a Najeriya, Dr. Usra Harahap, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.

Gwamnatin Indonesiya ta yi magana yayin da ta kai ziyara zuwa jihar Kebbi
Gwamantin Kebbi za ta taimakawa Kebbi wajen inganta kiwo, noma da samar da nama. Hoto: @AhmerdTata
Asali: Twitter

Gwamnatin Indonesiya ta ziyarci gwamnan Kebbi

Dakta Harahap ya ce manufar ziyarar ita ce kara karfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Indonesiya, Najeriya da jihar Kebbi, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 tana rufe, Gwamna ya bude wata babbar kasuwar dabbobi a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa ziyarar tana da nufin habaka hadin gwiwar da aka kulla tun farko tsakanin gwamnatin Kebbi da Indonesiya kan fasahar kiwo.

Jakadan ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen kafa cibiyoyin zamani na kiwo da samar da kayan sarrafa madara da nama a jihar.

Amfanin fasahar kiwo ga tattalin Kebbi

Hadin gwiwar za ta kuma tabbatar da inganta tsarin kiwo mai dorewa wanda zai haifar da karin samar da madara da nama cikin shekaru biyar masu zuwa.

Harahap ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar tare da samar da ayyukan yi ga mazauna Kebbi.

A nasa martanin, Gwamna Nasir Idris, wanda mataimakinsa, Alhaji Umar Abubakar-Tafida, ya wakilta, ya gode wa gwamnatin Indonesiya bisa wannan goyon baya mai muhimmanci.

Indonesiya: Limami ya rasu yana Sallah

A wani labarin, mun ruwaito cewa an ga wani bidiyon da ke nuna yadda wani limami ya yi kyakkyawar karshe yana tsaka da sallah a wani masallacin Indonesiya.

Bidiyon ya nuna lokacin da bawan Allah ya kwanta dama a lokacin da ya kai sujjada, wacce ta kasance ta karshe kenan a rayuwarsa lamarin da ya jawo mutane yi masa addu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel