Masu zanga-zanga sun lalata ofishin jakadancin Najeriya a Indonesia

Masu zanga-zanga sun lalata ofishin jakadancin Najeriya a Indonesia

Kusan mako guda bayan da wasu mutane suka rushe gine-gine a harabar ofishin jakadancin Najeriya a birnin Accra na kasar Ghana, wasu mutane sun maimaita makamancinsa a Indonesia.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wasu dimbin mutane sun kai hari ofishin jakadancin Najeriya da ke Jakarta, babban birnin Indonesiya.

An tattaro cewa, mutanen da suka kai wannan hari 'yan Najeriya ne masu zanga-zangar nuna bacin ransu a kan wariyar launin fata da take hakkinsu da jami'an shige da fice na Indonesiya suke yi.

A wasu faifan bidiyo da suka yadu a yanar gizo, an jiyo masu zanga-zangar dauke da alluna suna cewa, "Babu abinda Najeriya ta ke yi. Najeriya ba ta taimaka mana. Ba mu da ofishin jakadanci. Ba za mu yarda ba."

Ministan harkokin waje; Geoffery Onyeama, tare da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa; Yemi Osinbajo
Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Ministan harkokin waje; Geoffery Onyeama, tare da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa; Yemi Osinbajo Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Wasu daga cikinsu an hango suna lalata wata motar bas fara a harabar ginin ofishin jakadancin, yayin da wasu suka ragargaje kofofi da da tagogin ginin.

Masu zanga-zangar sun kuma ciro tutar Najeriya da ke harabar ofishin jakadancin, suna jan ta a kasa tare da yunkurin cinna mata wuta.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, a cikin wasu sakonni har kashi biyu da ya wallafa a kan shafinsa na Twitter, ya yi Allah wadai da harin a ranar Alhamis, yana mai bayyana hakan a matsayin "abin kunya".

KARANTA KUMA: Duk da matsin lambar da muke fuskanta ba za a buɗe makarantu ba a yanzu - Nwajiuba

Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da kokarin gano wadanda ake zargi da aikata wannan laifi.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da hare-hare har kashi biyu da aka kai ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin Kasar Ghana a makon jiya.

Wannan lamari ya sanya majalisar Wakilai ta ce dole ne Najeriya ta dauki mataki kan harin, domin irin wannan lamari ya fara wuce gona da iri.

Da yake magana a ranar Talata, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilan, ya ce nuna diflomasiya ta hanyar kawar da kai a kan lamarin ba zai magance matsalar ba.

Kalli faifan bidiyon da jaridar The Cable ta wallafa a kan shafinta na Twitter:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng