Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da aka yanke wa ‘Yan Najeriya 300

Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da aka yanke wa ‘Yan Najeriya 300

- Gwamnatin Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da ta yanke wa ‘yan Najeriya 50 da aka kama da miyagun kwayoyi a kasar

- Ta bukaci a yi masu rangwame zuwa daurin rai-da-rai a maimakon hukuncin kisa

- Akalla ‘yan Najeriya 300 ke jiran a aiwatar mu su da hukuncin kisa a kasashen Asia sakamakon samun su da laifin safarar miyagun kwayoyi

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da ta yanke wa ‘yan Najeriya 50 da aka kama da miyagun kwayoyi a kasar zuwa hukuncin daurin rai-da-rai

Ko da ya ke a dokar kasar Indonesia duk wanda aka kama da miyagun kwayoyi ko yana ta’ammali da ita ko kuma yana siyarwa hukuncin kisa ta rataya a wuyan shi.

KU KARANTA KUMA: Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci - Fadar Shugaban Kasa

Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da aka yanke wa ‘Yan Najeriya 300
Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da aka yanke wa ‘Yan Najeriya 300

Legit.ng ta tattaro cewa Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, ya gabatar da bukatar a wani ganawa da yayi da takwararsa ta Indonesia Retno Marsudi.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta kara kaimi wajen ganin an kubutar da ‘yan kasar da ke jiran a aiwatar mu su da hukuncin kisa.

Kungiyar LEDAP ta ce, akalla ‘yan Najeriya 300 ke jiran a aiwatar mu su da hukuncin kisa a kasashen Asia sakamakon samun su da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo mai taba zuciya da Legit.ng ta kawo maku

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng