'A Ji Ra'ayin Jama'a': Atiku Ya Magantu kan Kudirin Haraji, Ya ba Majalisa Shawara

'A Ji Ra'ayin Jama'a': Atiku Ya Magantu kan Kudirin Haraji, Ya ba Majalisa Shawara

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ba Majalisar Tarayya shawarwari kan kudirin haraji
  • Atiku ya bukaci sake duba abubuwan da ke cikin kudirin domin tabbatar da cewa sun dace da muradun yan Najeriya
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya kamata a yi duba kan shawarwarin da kwamitin tattalin arziki ya bayar game da kudirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan sabon kudirin haraji a Najeriya.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP ya shawarci yan Majalisa su tabbatar da abin da ke cikin kudirin ya dace da muradun yan Najeriya gaba daya.

Atiku ya yi magana kan sabon kudirin haraji a Najeriya
Atiku Abubakar ya ba Majalisar Tarayya shawara kan sabon kudirin haraji a kasar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Atiku ya fadi ra'ayinsa kan kudirin haraji

Atiku ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook da safiyar yau Lahadi 1 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Yan Arewa sun hada kai babu bambanci, sun taso Barau Jibrin gaba kan kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wazikrin Adamawa ya ce yan Najeriya sun hada kai wurin tabbatar da an yi adalci da kuma samun daidaito kan kudirin.

Atiku ya bukaci yan Majalisar Tarayya da su tabbatar da jin ra'ayin jama'a kan wannan kudiri a bayyane kuma cikin adalci.

Shawarar da Atiku ya bayar kan kudirin haraji

"Yan Najeriya sun hada kai game da harkar kudi da zai tabbatar da adalci da daidaito ba tare da fifita wasu jihohi ba da kuma hukunta wasu."
"Ina bukatar a gudanar da adalci da gaskiya wurin kaddamar da jin ra'ayin jama'a a Majalisar, na yi imanin yin haka zai kawo shugabanci nagari da sanya yarda a zukatan al'umma ga tsare-tsaren gwamnati."
"Ya kamata Majalisar ta sake duba abubuwan da ke cikin kudirin domin tabbatar da cewa ya dace da muradun mafi yawan yan Najeriya."

- Atiku Abubakar

Atiku ya kuma bukaci Majalisar ta duba shawarar da kwamitin tattalin arziki ya bayar a matsayinsa na mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

'Za ku yabawa Tinubu nan gaba': Dan Majalisar Tarayya daga Arewa kan kudirin haraji

Dan Majalisar ya yabi Tinubu kan haraji

Kun ji cewa ana ta hayya-hayya kan kudirin haraji a Najeriya, dan Majalisar Tarayya ya yabawa Bola Ahmed kan kokarinsa.

Hon. Philip Agbese daga jihar Benue ya ce yan Najeriya za su zo daga baya suna yabon Tinubu saboda irin tsare-tsaren da ya kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.