Ana Murna Gwamna Ya Amince a Biya Ma'aikata Albashin Watan 13

Ana Murna Gwamna Ya Amince a Biya Ma'aikata Albashin Watan 13

  • Ma'aikatan jihar Edo za su samu ƙarin albashi na watan 13 sakamakon matakin da Gwamna Monday Okpebholo ya ɗauka
  • Gwamna Monday Okpebholo ya amince a biya ma'aikatan jihar albashi na watan 13 domin ƙara musu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu
  • Monday Okpebhoo ya kuma amince da ɗaukar ɗaliban jihar waɗanda suka kammala digiri da sakamako mafi kyau aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya amince a biya ma'aikata ƙarin albashi.

Gwamna Okpebholo ya amince a biya ma'aikatan jihar albashi na watan 13.

Gwamnan Edo ya amince a biya ma'aikata albashi
Gwamnan Edo ya amince a ba ma'aikata albashi na watan 13 Hoto: @MondayOkpebholo
Asali: Facebook

Shugaban ma'aikatan jihar, Anthony Okungbowa ya bayyana hakan a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Edo zai ba ɗalibai aiki

Gwamna Okpebholo ya kuma amince da tsarin ɗaukar ɗalibai ƴan jihar Edo daga kowace jami'a a Najeriya da ƙasashen waje, da suka kammala digiri da sakamakon da yafi kowane aiki kai tsaye, rahoton Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya amince da mafi karancin albashi, ya fadi abin da zai biya ma'aikata

Shugaban ma'aikatan Anthony Okungbowa, ya ce shirin ɗaukar ɗaliban aiki, an ɓullo da shi ne domin tabbatar da an ɗauki ingantattun ma'aikata aiki.

"Mai girma gwamna yana yin hakan ne domin ƙarfafa gwiwar ma'aikata su ci gaba da yin iyakar bakin ƙoƙarinsu."
"Gwamna ya amince da shirin bunƙasa ɗaliban da suka kammala karatu wanda ya haɗa da ɗaukar waɗanda suka samu sakamako mafi kyau a matsayin ma'aikata, da nufin ƙara bunƙasa ayyuka."

- Anthony Okungbowa

Karanta wasu labaran kan jihar Edo

Gwamnan Edo ya rushe sababbin masarautu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya rusa dokar masarautu da tsohuwar gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira.

Gwamna Okpebholo ya rusa masarautun ne inda ya dawo da ainihin ikon Oba na Benin, Oba Ewuare II a jihar bayan rage masa kima a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng