Abin da Ƴan Bindiga Suka Faɗawa Gwamnan Kaduna Kafin Su Tuba Su Miƙa Wuya
- Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana yadda gwamnatisa ta tattauna da ƴan bindiga kafin su miƙa wuya a Birnin Gwari
- Uba Sani ya vlce ƴan tubabbun ƴan bindigar sun shaida masu cewa jami'an tsaro sun hallaka da dama daga cikinsu
- Ya ce gwamnatinsa za ta fara tattara bayanan dukkan tubabbun ƴan bindiga waɗanda suka miƙa wuya a jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Malam Uba Sani ya yi bayanin yadda tattaunawar gwamnatinsa da ƴan bindiga ta kaya gabanin su tuba su miƙa makamansu a jihar Kaduna.
Mai girma gwamnan Kaduna ya ce gwamnati za ta fara tattara bayanan tubabbun ƴan bindiga daga ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba, 2024.
Gwamna Uba Sani ya faɗi haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels tv a cikin shirin nan na su mai taken, 'siyasa a yau'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ranar Alhamis da ta gabata, Gwamna Uba Sani ya karɓi rukunin farko na tubabbun ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
Abin da ƴan bindiga suka faɗawa gwamna
Daily Trust ta tattaro cewa yayin tattaunawa da shi, gwamnan Kaduna ya ce galibin ƴan bindigar da ke ta'addanci a Birnin Gwari a nan aka haife su.
Uba Sani ya ce:
"Mun yi doguwar tattaunawa da wasu daga cikinsu, sun tabbatar mana da cewa jami'an tsaro sun hallaka ƴan uwansu ƴan bindiga da dama.
"Ba mu ba su ko ƙwandala ba, babu batun kudi a tattaunawar mu da su, dama duk sun gaji da aikata miyagun laifuka. Ni ina ganin idan aka daina saka siyasa a sha'anin tsaro komai zai wuce."
Za a fara ɗaukar bayanan tubabbun miyagu
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta haɗa kai da hukumomin tsaro da ofishin mai ba da shawara kan tsaron kasa kafin ta kai ga samun wannan nasara.
"Wannan shi ne tsarin Kaduna, ya bambanta da ko'ina. Daga gobe (Asabar), za mu fara rajistar mafi yawan wadannan mutanen da suka tuba."
Ƴan sanda sun kama miyagu 523 a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta yi nasarar kama tarin miyagu da suka aikata laifuffuka daban daban a fadin jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama yan ta'adda da sauran bata gari 523 da suka hada da masu garkuwa da mutane
Asali: Legit.ng