Kano: Ganduje da Aminu Ado Sun Bude Masallacin Juma'a, an Musuluntar da Mutane
- Gidauniyar Abdullahi Ganduje ta bude sabon masallacin Juma'a da makarantar Islamiyya domin koyar da addini
- Shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado su suka jagoranci bude masallacin a yau Juma'a
- Taron ya samu halartar manyan yan jam'iyyar APC da kuma shugabanni da malaman addinin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun jagoranci bude sabon masallacin Juma’a a jihar.
Ganduje da Aminu Ado Bayero sun buɗe makarantar Islamiyya da Gidauniyar Ganduje ta gina ne a unguwar Gidan Goje da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Gidauniyar Ganduje ta Musuluntar da mutane 400
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Ganduje a bangaren sadarwa ta zamani, Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a shafinta Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta tabbatar da cewa kimanin mutane 400 daga kabilar Maguzawa suka karbi addinin Musulunci a karamar hukumar.
Wannan al’amari ya kasance wani muhimmin nasara wajen yada addinin Musulunci da cusa fahimtar addinin Musulunci a zukatan al’umma.
Manyan baki da suka halarci taron bude masallaci
Taron ya samu halartar manyan malamai da suka hada da Shugaban Kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakataren Kungiyar, Sheikh Kabiru Gombe.
Sannan akwai shugaban hukumar NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da kuma Wakilin Sheikh Karibullah Nasiru Kabara da sauran fitattun malamai.
Bugu da kari, Dr. Ganduje ya samu rakiyar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da sakataren jam’iyyar na kasa, Ajibola Basiru.
Sai kuma mai ba da shawara a bangaren shari’a, Farfesa Abdulkareem Kana da tsohon dan takarar mataimakin gwamna a Kano, Murtala Sule Garo.
Ganduje ya raba kujerun hajji a Kano
Kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi goma ta arziki ga wadanda suka lashe gasar karatun Alkur'ani a jihar Kano.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mahaddatan Alkur'ani sun samu kyaututtukan da suka hada da kujerun Hajji da ababan hawa.
Asali: Legit.ng