Shettima, Jonathan da 'Yan Siyasa Sun Halarci Birne Matar Gwamna, Hawaye Sun Zuba
- Bola Tinubu ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima a bikin birne matar Gwamna Umo Eno a Akwa Ibom
- An gudanar da bikin birne matar gwamnan ne mai suna Fasto Patience Eno a yau Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024
- Wannan na zuwa ne bayan Fasto Patience Eno ta rasu a ranar 27 ga watan Satumbar 2024 da muke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Manyan yan siyasa a Najeriya sun halarci bikin birne matar gwamna Eno Umo na Akwa Ibom.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya wakilci Bola Tinubu yayin bikin a yau Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024.
Shettima ya halarci bikin birne matar gwamna
Hadimin Shettima a bangaren sadarwa, Stanley Nkwocha shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nkwocha ya ce Shettima ya halarci bikin birne marigayiya, Patience Eno a karamar hukumar Nsit Ubium da ke jihar.
Mataimakin shugaban kasar ya wakilci Tinubu ne yayin da shugaban ke ziyarar aiki a kasar Faransa.
An yabawa matar gwamna Edo da ta mutu
Kashim ya ce marigayiyar ta taka muhimmiyar rawa wurin inganta rayuwar al'umma inda ya ce rayuwarta abin koyi ne ga sauran yan kasa.
Har ila yau, ya ce marigayiyar ta zama garkuwa ga mijinta da kuma iyalanta wacce za a yi jimamin rashinta matuƙa musamman a jihar.
Sauran 'yan siyasa da suka halarci jana'iza
'Yan siyasa da suka halarci akwai shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau I. Jibrin.
Sauran sun hada da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da mataimakin kakakin Majalisa, Hon. Benjamin Kalu da sauransu.
Matar gwamnan Akwa Ibom ta rasu
Kun ji cewa Allah ya karbi rayuwar uwar gidan gwamnan Akwa Ibom, Fasto Misis Patience Umo Eno a wani asibiti bayan fama da rashin lafiya.
Kwamishinan yada labarai, Mista Ini Ememobong ya fitar da sanarwar rasuwar inda ya ce ta rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga Satumba.
Duk da rasuwar matarsa, sanarwar ta ce Gwamna Umo Eno ya ba al'ummar Akwa Ibom tabbacin jajircerwarsa wajen yi masu hidima.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng