Kotu Ta Saki Mutane 50 da Ake Zargin 'Yan Haramtacciyar Kungiyar IPOB ne

Kotu Ta Saki Mutane 50 da Ake Zargin 'Yan Haramtacciyar Kungiyar IPOB ne

  • Babbar kotun tarayya ta wanke wasu da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne daga tuhume-tuhumen gwamnati
  • Rundunar 'yan sanda ta kasa ce ta gurfanar da mutanen a gaban Mai Shari'a, James Omotosho kan zargin ta'addanci
  • A hukuncin da ya zartar, Alkalin babbar kotun ya fadi dalilin da ya sa ya wanke wadanda ake zargi da laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ba da umarnin sakin mutane 50 da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne.

Haka kuma kotun ta wanke dukkanninsu daga zargin ta’addanci da gwamnatin Najeriya ke zargin ta kama su da aikatawa.

Abuja
Kotu ta wanke mutane 50 daga zargin ta'addanci Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana dalilin da ya sa kotu ta saki mutanen.

Kara karanta wannan

An gurfanar da surukin Buhari a kotu, ana zargin ya karkatar da kudin jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta saki 'yan kungiyar IPOB a Najeriya

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Mai Shari'a, James Omotosho ya ce, rundunar ‘yan sanda ta gaza gabatar da wata hujja mai inganci kan mutanen da ake tuhuma da ta'addanci.

Alkalin kotun ya kara da cewa wannan ce ta sa ya yi watsi da tuhume-tuhume uku da rundunar 'yan sandan kasar nan ta gabatar gabansa.

Zargin da ake wa 'yan kungiyar IPOB

Ana zargin mutanen da taruwa a cikin wata mota mai rajista XA-139 BDN da zimmar aikata wani aikin ta’addanci. Ana kuma zargin su da mallakar wasu abubuwan tsafi da launin huluna da ke nuna fafutukarsu ta kokarin ballewar daga Najeriya.

'Yan IPOB sun budewa sojoji wuta

A baya mun ruwaito cewa wasu miyagun mutane dauke da bindigu, sun budewa sojojin Najeriya da ke Abia wuta, wanda ya jawo gagarumar asara ga rundunar sojojin kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sauya magana, ta fadi mamallakin shinkafar 'Tinubu' da aka kama

'Yan IPOB sun kai harin ne a lokacin da ta ke bikin ranar tunawa da kokarinta na samar da kasar Biafra, tare da ballewa daga Najeriya, lamarin da gwamnati ta ki amincewa da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.