Jerin Kasashe 5 da ba Su da Sojoji, 'Yan Sanda da Sauran Jami'an Tsaro

Jerin Kasashe 5 da ba Su da Sojoji, 'Yan Sanda da Sauran Jami'an Tsaro

Ƙasashe da dama na maida hankali wajen samar da hukumomin tsaro na sojoji, ƴan sanda da sauransu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Samar da hukumomin tsaro na tabbatar da wanzar da zaman lafiya tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Kasashen da ba su da sojoji
Iceland na daga cikin kasashen da ba su da sojoji a duniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wasu ƙasashen ba su da jami'an tsaro

Sai dai, duk da muhimmancin da hukumomin tsaro suke da shi, ba kowane ƙasashe ba ne suke da su, cewar rahoton TimesofIndia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan ƙasashen waɗanda ba su da yawa, suna samun zaman lafiya ba tare da jami'an tsaro na su na kansu ba.

Ta wace hanya kasashen suke samun tsaro?

Ƙasashen sun dogara da tsare-tsare na musamman, kamar ƙawance da wasu ƙasashe domin kiyaye lafiyar ƴan ƙasarsu. 

Yawancin ƙasashen waɗanɗa ba su da jami'an tsaro, ba su da yawan mutane kuma ba a cika aikata laifuka ba.

Kara karanta wannan

NDLEA ta yi babban kamu, dan kasuwar da ya shigo da hodar iblis ya shiga hannu

Ƙasashen da ba su da sojoji da ƴan sanda

Ga jerin ƙasashen da ba su da sojoji ko ƴan sanda:

1. Iceland

Ƙasar Iceland da ke a nahiyar Turai, ta yi fice a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ba su da sojoji.

Shafin Statistics Iceland ya bayyana cewa ƙasar tana da yawan mutane 383,726 a farkon shekarar 2024.

Iceland tana dogara da kasancewarta 'yar ƙungiyar NATO da ƙawancenta da ƙasar Amurka, domin samun kariya idan buƙatar hakan ta taso.

Ƙasar Iceland tana daga jerin ƙasashe mafiya zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, cewar rahoton

2. Liechtenstein

Liechtenstein ƙaramar ƙasa ce mai zaman lafiya wacce ke a tsakanin ƙasashen Switzerland da Austria.

Ƙasar Liechtenstein ta soke sojojinta a shekarar 1868 saboda tsadar kula da su.

Liechtenstein ta dogara da ƙasar Switzerland wajen samun taimako idan buƙatar hakan ta taso, saboda dangantaka mai kyau da ke a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawa ciki har da jariri a Zamfara

3. Vatican

Vatican, wacce ita ce ƙaramar ƙasa mai cin gashin kanta a duniya, ba ta da sojoji ko ƴan sanda.

A maimakon hakan, tana samun tsaro daga rundunar Swiss Guard, wata ƙwararriya tawaga wacce gwamnatin Switzerland ta samar, wanda mambobinta suka yi rantsuwar kare Fafaroma.

Vatican ta kuma dogara da sojoji da ƴan sandan Italiya domin ƙara samun tsaro.

4. Monaco

Monaco, wata ƴar ƙaramar ƙasa ce da ke a gaɓar French Riviera, wacce ba ta da sojoji.

A maimakon hakan, tsaron Monaco ya rataya ne a kan wuyan ƙasar Faransa, wacce ke da yarjejeniyar kare ƙasar idan buƙatar hakan ta taso.

5. Andorra

Ƙasar Andorra wacce ke a tsakanin ƙasashen Faransa da Spain ba ta da sojoji.

Ƴar ƙaramar ƙasar tana dogara ne a kan ƙasashen Faransa da Spain domin samun kariya.

Ƙasashen guda biyu masu makwabtaka da ita, suna kulawa da duk wata barazana kan tsaronta.

Kara karanta wannan

Jerin ƙasashe 7 da ba a biyan haraji yayin da ake surutun sabon kudirin haraji a Najeriya

Shafin andorapartner ya bayyana cewa ƙididdigar da majalisar ɗinkin duniya ta yi, ta baya-bayan nan ta nuna cewa akwai ƙarancin aikata laifuka a ƙasar.

Ƙididdigar ta nuna cewa an samu mutum 153.9 da laifi a cikin mutane 100,000.

FBI ta cafke wanda ya farmaki sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta sanar da kama Anas Said, wanda ake zargi da shirya harin ta’addanci kan sojojin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa Anas Said ne ya kitsa yadda aka farmaki sojojin a shingensu na binciken ababen hawa da ke jihar Borno a shekarar 2023.

Ayyukansa sun ja hankalin duniya sosai, sakamakon alakar da ake zargin ya na da ita da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi na duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng