Kasashen duniya 8 mafi karfin Soja a duniya a 2021 (Jerinsu)

Kasashen duniya 8 mafi karfin Soja a duniya a 2021 (Jerinsu)

- Kowace kasa na alfahari da adadin Sojojin da take shi da makamai

- Yayinda wasu ke tunanin Amurka ta fi kowa karfi, kasar Sin ta zarce mata

Wani jerin kasashe masu karfin Soja a duniya a 2021 da Global Firepower ta saki ya nuna cewa kasar Sin ne kan kan gaba wajen yawan jami'an sojoji, rahoton Statista ta bayyana.

Rahoton ya nuna cewa kasar sin na adadin Sojoji milyan 2.19 dake shirye da fuskantar yaki. Kasar da ta samu damar zuwa ta biyu itace Indiya mai adadin Sojoji milyan 1.45.

Amurka ce ta zo na uku da Sojoji milyan 1.4, sannan sai kasar Koriya ta Arewa.

Ga jerin kasashe 8 mafi karfin Soja a duniya:

1. Sin: 2,185,000

2. Indiya: 1,445,000

3. Amurka: 1,400,000

4. Korea ta Arewa : 1,300,000

5. Rasha: 1,014,000

6. Pakistan: 654,000

7. Korea ta kudu: 600,000

8. Iran: 525,000

KU DUBA: Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)

Kasashen duniya 8 mafi karfin Soja a duniya a 2021 (Jerinsu)
Kasashen duniya 8 mafi karfin Soja a duniya a 2021 (Jerinsu) Photo CreditL Statista
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona

Legit.ng ta lura cewa babu kasar Afrika ko daya cikin manyan kasashe 8 mafi karfin Soja.

Amma a 2019, Sojojin Najeriya sun zo na hudu a jerin Soji mafi karfi a nahiyar Afrika.

A bisa rahoton da Global Firepower ya saki, Najeriya ta biyo bayan Misra, Aljeriya, da Afrika ta kudu.

A duniya kuwa, Najeriya ta zo na 44 a shekarar 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel