Kudirin Haraji: Sheikh Mansur Sokoto Ya Ba 'Yan Majalisa Shawara Ana Zargin Maƙarƙashiya

Kudirin Haraji: Sheikh Mansur Sokoto Ya Ba 'Yan Majalisa Shawara Ana Zargin Maƙarƙashiya

  • Kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke gaban majalisa na cigaba da shan suka musamman daga Arewacin Najeriya
  • Shahararren malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya bukaci yan majalisa su yi taka tsantsan game da kudirin
  • Hakan na zuwa ne bayan kudirin ya tsallake karatu na daya a majalisar dattawan Najeriya a ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Malaman addini a Najeriya na cigaba da magana a kan kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto MON ya ce akwai bukatar a kammala tantance kudirin kafin a tabbatar da shi.

Mansur Sokoto
Malamin addini ya bukaci a yi taka tsan tsan kan kudirin haraji. Hoto: Mansur Sokoto
Asali: Facebook

Legit ta tattaro maganganun da malamin ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Dokar Haraji: Sanatocin Arewa sun yi ganawar sirri bayan kudirin ya tsallake karatu na 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mansur Sokoto da kudirin harajin Tinubu

Sheikh Mansur Sokoto ya ce hankulan al'umma ba zai kwanta ba idan suka ga ana gaggawar tabbatar da wani kudiri.

Shehin malamin ya yi magana ne bayan majalisa ta yi karatu na daya ga kudirin haraji alhali ana tsaka da ce-ce-ku-ce a kansa.

Farfesa Mansur Sokoto ya bukaci yan majalisa su tabbatar da tantance kudirin kafin amincewa da shi.

"Duk lokacin da muka ga ana gaggawar tabbatar da wata doka ba tare da an bi ka'idoji an tantance alfanunta, an saurari ra'ayoyin masana kuma an yi gyaran da ya dace ba.
Muna da haƙƙin mu yi zargin akwai wata almundahana ko maƙarƙashiya a cikin ta.
Mu na ba 'yan majalisunmu shawara su yi takantsantsan daga sa hannu ga duk wani ƙudiri da ba a tantance shi yadda ya kamata ba."

- Farfesa Mansur Sokoto

A yanzu haka dai kallo ya koma kan 'yan majalisar dattawa da dokoki domin ganin matakin da za su dauka a kan kudirin.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta tafka muhawara, kudirin harajin Tinubu ya tsallake karatu na 2

An yi hargitsi a majalisa kan kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta shiga hargitsi yayin da aka zo bayani kan kudirin harajin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

An gayyato shugabannin FIRS da na DMO domin su yi bayani ga majalisar a kan manufofin kawo kudirin haraji da shugaba Tinubu ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng