Gasar Alkur'ani: Khadimul Islam, Ganduje Ya Raba Kujerun Hajji da Motoci

Gasar Alkur'ani: Khadimul Islam, Ganduje Ya Raba Kujerun Hajji da Motoci

  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi goma ta arziki ga wadanda suka lashe gasar karatun Alkur'ani a jihar Kano
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mahaddatan Alkur'ani sun samu kyaututtukan da suka hada da kujerun Hajji da abubuwan hawa
  • Taron ya samu halartar manyan mutane a Najeriya ciki har da shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - An kammala gasar karatun Alkur'ani da gidauniyar Abdullahi Ganduje ta shirya a Kano.

Shugaba APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya raba manyan kyaututtuka ga waɗanda suka lashe gasar.

Ganduje
Ganduje ya raba kujerun Hajji yayin gasar Alkur'ani. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a Facebook cewa gidauniyar Ganduje ta shafe sama da shekaru 30 tana gudanar da irin ayyukan a Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kotu ta fatattaki shugabannin da Ganduje ya naɗa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ganduje ya raba kujerun Hajji a Kano

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya raba kyautar kujerun Hajji ga wadanda suka shiga sahun farko a gasar Alkur'ani.

Haka zalika yan sahun farko a matakai daban daban sun samu kyautar motoci da Keke NAPEP daga gidauniyar Ganduje.

Dr. Ganduje ya raba babura da keken dinki

Sauran mahaddatan da suka fafata a gasar sun samu kyautar babura daga Abdullahi Umar Ganduje.

Haka zalika an rabawa wasu daga cikin mahaddatan da suka shiga gasar kyautar keken dinki da keken hawa.

Manyan baki da suka halarci gasar Kur'ani

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Abdulwahab Abdallah.

Mataimakin dan takarar gwamnan APC a Kano a 2023, Murtala Sule Garo da Asiya Abdullahi Ganduje na cikin waɗanda suka mika kyauta ga mahaddatan.

Abdullahi Ganduje ya ce yana shirya gasar karatun ne domin karfafa dalibai su rika haddar Alkur'ani mai girma.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe dattijo mai shekaru 85 bayan karɓar kudin fansa

An bude gasar karatun Alkur'ani a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da Naira miliyan 130 domin daukar nauyin gasar karatun Al-Kur'ani.

Gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed ne ya sanar da cewa ya ba da izinin fitar da kudin a taron bude gasar da aka gudanar a Jama'are.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng