Tinubu Ya Samu Matsala a Arewa, Zulum Ya Shirya Yaƙar Dokar Sake Fasalin Haraji
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya soki dokar sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya kai majalisar tarayya
- Farfesa Zulum ya ce dokar za ta jawo koma baya ga Arewa da wasu jihohin Kudancin Najeriya don haka akwai bukatar soke ta
- Gwamnan ya yi kira ga 'yan majalisa da su yi hattara, su tsaya tsayin daka, su tabbatar da cewa ba za a amince da dokar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi Allah wadai da dokar sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya kai majalisa.
Babagana Zulum ya ce sabuwar dokar ba alheri ba ce ga jihohin Arewa da wasu jihohin Kudu, yana mai nuna adawarsa da dokar a fili
"Mun yi tir da dokar haraji" - Gwamna Zulum
A wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC, gwamnan jihar na Borno ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi tir da wannan dokar da aka kai majalisar tarayya, zai kawo koma baya ga Arewa, da jihohin Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, Kudu maso Yammma.
"Wannan ba adawa ba ce, wannan wani abu wanda mu a ganinmu zai kashe Arewa gaba daya, saboda haka mun kira Shugaba Bola Tinubu ya duba wannan lamari.
"Mu abinda muke so yanzu, maganar dokar harajin nan, kar a yi."
"Menene ya kawo hanzarin shigar da dokar?" Zulum
Farfesa Babagana Zulum, ya nuna damuwarsa kan yadda shugaban kasar ke hanzarin ganin majalisar tarayya ta zartar da sabuwar dokar sabunta haraji.
"Akwai kudurin dokar man fetur da aka kai wa majalisar, yana nan kusan shekaru 20 kafin aka zartar da shi, me ya sa ake hanzarin zartar da dokar harajin?
"Mu muna cewa ayi hankali a duba, a tabbatar cewa wannan abun ko mu bama nan yaranmu za su amfana."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Gwamnan ya nuna cewa ko da majalisar tarayya ta amince da dokar, gwamnoni ba za su iya biya ba, ya ce ko an biya yanzu to nan da shekara daya zai zama masifa.
Zulum ya aika sako ga 'yan majalisa
A yayin da ya jaddada cewa sabuwar dokar harajin za ta jawo koma baya ga Arewa da wasu jihohin Kudu, Zulum ya yi kira ga 'yan majalisar tarayya.
"Wannan abin bai nuna cewa muna adawa da gwamnati ba, wannan abin ra'ayinmu ne domin zai mayar da mu baya kamar yadda muka gani.
"Kuma na kira dukkanin 'yan majalisar dattawa da na wakilai da kar da su yarda da dokar, su zauna daram, kuma kar kowa ya sayar da mu, ayi hankali.
"Kar wani ya zo ya ce maku shugaban kasa ya ce ayi haka, ba haka ba ne, wannan siyasa ce, mun jefa masa kuri'a, ba mu ce wani abu ba, amma wannan dokar ba zai fitar da mu ba."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Kalli bidiyon tattaunar a kasa:
Sanatocin Arewa sun shiga ganawar sirri
A wani labarin, mun ruwaito cewa sanatocin Arewa sun shiga wata ganawar sirri a zauren majalisar tarayya kan dokar gyaran haraji da ta tsallake karatu na biyu.
Shugaban kungiyar sanatocin Arewa, Abdulaziz Yar'Adua bai bayyana dalilin ganawar ba amma ana tunanin sun tattauna ne kan dokar harajin da ta jawo ce-ce-ku-ce.
Asali: Legit.ng