Bayanai Sun Fito da Kotu Ta Garkame Ƴan Sanda 2 da Jami'in Hukumar NIS a Gombe

Bayanai Sun Fito da Kotu Ta Garkame Ƴan Sanda 2 da Jami'in Hukumar NIS a Gombe

  • Babbar kotun tarayya a Gombe ta yanke hukuncin shekaru bakwai ga ‘yan sanda biyu da jami’in NIS kan damfarar N1.6m
  • An tuhumi Yusuf Abdulkarim Bature da Musa Philip da karbar N970,000, yayin da Nasiru Mohammed ya karbi N670,000
  • Kotun ta umurce su da su biya diyyar N1.64m ga wadanda suka damfara, sannan ta basu zabin biyan tara idan ba sa son dauri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Wata babbar kotun tarayya a Gombe ta yanke wa ‘yan sanda biyu da jami’in shige da fice hukuncin daurin shekaru bakwai saboda damfarar N1.6m.

Hukumar EFCC ta gurfanar da 'yan sandan, Yusuf Abdulkarim Bature da Musa Philip kan tuhume biyu na karbar kudi ta hanyar yaudara da nufin damfara.

Kara karanta wannan

Badakalar N110bn: EFCC ta gaza gurfanar da tsohon gwamnan Kogi a gaban kotu

Babbar kotun tarayya a Gombe ta garkame 'yan sanda biyu da jami'in hukumar NIS
'Yan sanda biyu da jami'in NIS sun amsa laifin damfara, kotu ta kulle su shekaru 7. Hoto: Federal High Court
Asali: UGC

Ana zargin jami'an tsaro da damfara

Nasiru Mohammed, jami’in shige da fice, shi ma an gurfanar da shi kan tuhuma daya na karbar kudi ta hanyar yaudara, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar karar, Bature da Philip sun karbi N970,000 daga Asabe Hamed a 2022 da nufin sama mata aiki, duk da cewa sun san karya suke yi.

Hakazalika, an zargi Nasiru Mohammed da karbar N670,000 daga Abdul Rahman Abubakar da Akwalo Adamu da zummar sama masu aiki a hukumar NIS.

Jami'an 3 sun amfa laifin damfara

EFCC ta bayyana cewa karbar kudaden da suka yi ya saba wa dokar 'Damfarar karbar kudi kafin aiki da sauran dangogin damfara ta 2006.'

A lokacin zaman kotu, dukkanin wadanda ake tuhuma sun amsa laifinsu, inda suka tabbatar da aikata abin da ake zarginsu da shi.

Bayan amincewar laifinsu, lauyan EFCC, Tortema Joshua, ya bukaci kotu ta yanke musu hukunci bisa abin da doka ta tanada.

Kara karanta wannan

'An kashe mutum 24, an cafke 1,200': Amnesty ta saki rahoton zanga zangar Agusta

Kotu ta daure jami'an shekaru bakwai

Sai dai lauyoyinsu, Babangida Mohammed da K.K. Jomoh, sun roki kotu da ta yi musu sassauci, duba da yadda suka nuna nadama.

Mai shari’a T.G. Ringing ya yanke musu hukuncin shekaru bakwai a kurkuku ko zabin biyan tara na N50,000 kowannensu.

Bugu da ƙari, kotu ta umarce su da su biya diyyar N1.64m ga wadanda suka yi wa damfara tare da sa hannu kan alkawarin zama cikin kyakkyawar ɗabi’a nan gaba.

Alkalin kotu ya garkame shugaban 'yan sanda

A shekarar 2022 ne Legit Hausa ta rahoto cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta garkame shugaban ‘yan sanda, Usman Alkali Baba na watanni uku a gidan yari.

Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da wani jami'in dan sanda mai suna Patrick Okoli ya shigar bisa zargin shugaban 'yan sandan da yi masa ritayar dole ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.