An Shiga Tashin Hankali a Kudu, 'Yan Daba Sun Yi Awon Gaba da Sandar Majalisa

An Shiga Tashin Hankali a Kudu, 'Yan Daba Sun Yi Awon Gaba da Sandar Majalisa

  • Rigima ta barke a majalisar karamar hukumar Abeokuta da ke jihar Ogun kan zaben shugabanni ta hanyar kada kuri’a
  • Ana tsaka da wannan rigimar ne wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne suka kutsa majalisar tare da sace sandar girma
  • Shugaban majalisar ya zargi shugaban karamar hukumar Lanre Oyegbola da hannu a haddasa rikcin da kuma sace sandar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - An rahoto cewa taron rantsar da majalisar dokoki ta karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun ya rikide zuwa tashin hankali.

Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daba sun sace sandar girma ta majalisar, inda ake zargin shugaban karamar hukumar, Lanre Oyegbola ne ya sanya su.

Shugaban majalisar karamar hukuma a Ogun ya zargi ciyaman da hannu a sace sandar girma
'Yan daba sun yi awon gaba da sandar majalisar karamar hukuma a Ogun.
Asali: UGC

Rikici ya barke a taron majalisar Abeokuta

Moruf Erubami ya zama shugaban majalisar ba tare da hamayya ba, amma rikici ya barke lokacin da kansiloli suka nace sai sun kada kuri’ar zaben sauran shugabanni, inji Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 18, gwamnatin tarayya ta sanya ranar gudanar da ƙidaya a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyegbola, wanda kwanan Gwamna Dapo Abiodun ya rantsar da shi da sauran ciyamomin kananan hukumomi 19 na wurin taron da aka yi a sakatariyar Akomoje, Abeokuta.

An fara ce-ce-ku-ce bayan da majalisar da ke da kansiloli 16 ta rabu gida biyu, inda kansiloli tara suka nuna gaba da sauran bakwai, lamarin da ya hargitsi wurin.

An yi awon gaba da sandar majalisa

Bayan jawabin Erubami, an ce ‘yan sanda da ake zargin suna tare da shugaban karamar hukumar sun fara harbi a wajen majalisar, wanda ya jefa jama’a cikin rudani.

An ce shugabannin APC na yankin sun ranta a na kare lokacin da matasa masu biyayya ga Oyegbola sun kutsa majalisar tare da sace sandar iko.

Erubami ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi Oyegbola da hannu wajen satar sandar girma don hana zaben sauran shugabanni ta hanyar kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Kotu Ta kori ƙarar da aka nemi hana EFCC kama gwamna idan ya bar mulki a 2027

Kokarin jin ta bakin Oyegbola ya ci tura, domin bai amsa kiran waya ba, kuma bai mayar da sakonnin kar ta kwana da na WhatsApp ba.

An kai hari majalisar dokokin Ogun

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu yan dabar siyasa sun kai hari majalisar dokokin jihar Ogun kuma sun yi awon gaba da sandar iko ta majalisar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce 'yan dabar sun sace sandar ne da sanyin safiya, amma an gano kanta ba tare da gano inda gangar jikinta take ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.