Lokuta 6 da aka taba sace sandar girma a majalisun Najeriya

Lokuta 6 da aka taba sace sandar girma a majalisun Najeriya

Wani abun al'ajani da 'yan Najeriya suka tashi da shi a ranar Larabar da ta gabata shine yadda wasu katti suka shiga majalisar dattijan Najeriya suka kuma yi awon gaba da sandar girman majalisar da karfi da yaji.

Sai dai majalisar ta zargi Sanatan nan da ta kora har na tsawon kwanaki 90 Sanata Ovie Omo-Agege da jagorantar kattin domin hargitsa zaman majalisar.

Lokuta 6 da aka taba sace sandar girma a majalisun Najeriya
Lokuta 6 da aka taba sace sandar girma a majalisun Najeriya

KU KARANTA: An gano alakar Buhari da babban Bishof din Ingila

Legit.ng haka zalika ta tattaro ma masu karatun mu wasu lokuta a baya da aka taba sace sandar girma a majalisun kasar.

1. A shekarar 1965 a Majalisar Wakilan shiyyar jihar Yamma a jamhuriya ta farko inda Mista Ebubedike da ke wakiltar yankin Badagry ta Gabas ya dauke sandar majalisar.

2. Marigayi Chuba Okadigbo ma ya taba dauke sandar girman a shekarar 2000 bayan dangantakar sa tayi tsami tsakanin sa da shugaban kasa Cif Obasanjo.

3. Majalisar Dokokin Jihar Ribas ba an taba dauke sandar a shekarar 2013 biyo bayan zazzafar gaba da ta barke tsakanin gwamnan jihar a wancan lokacin Cif Rotimi Amaechi da kuma gwamnan jihar na yanzu Mista Nyesom Wike.

4. Haka ma dai a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a sace sandar duk dai a shekarar 2013 biyo bayan hatsaniya a majalisar da ta kai ga tsige shugaban majalisa na lokacin Alhaji Usman Gangara, da sauran shugabannin majalisar.

5. Haka zalika a Majalisar Dokokin jihar Anambara ma a shekarar da ta gabata ta 2017 an sace sandar inda aka zargi shugabar majalisar dokokin jihar Misis Rita Maduagwu da yin gaba da sandar yayin da 'yan majalisar suka yi kokarin tsige ta.

6. A ranar Larabar da ta gabata biyo bayan dakatarwar da aka yi wa dan majalisar dattijai Sanata Ovie Omo-Agege.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng