Ban da Zanga Zanga: Osinbajo Ya Fadi Hanya 1 da Matasa Za Su Kawo Canji a Najeriya

Ban da Zanga Zanga: Osinbajo Ya Fadi Hanya 1 da Matasa Za Su Kawo Canji a Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jaddada cewa shiga harkokin siyasa na samar da mafita fiye da zanga-zanga
  • Yayin da kafofin sada zumunta ke taka rawa wajen fadin albarkacin baki, Osinbajo ya nuna muhimmancin sa ido kan gudanarwarsu
  • Shugaban ya yi kira ga matasa da su shiga cikin harkokin siyasa domin kawo sauyi mai dorewa, musamman a kasashen da ke ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce wajibi ne a daina kallon zanga zanga a matsayin abu daya tilo da zai kawo sauyi a siyasar kasashen da ke ci gaba.

Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wani taro kan fasaha, sababbin kafafen yada labarai da gwamnati da aka gudanar a Gbagada, jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Yakubu Gowon: Abin da yake ci mani tuwo a kwarya game da matsalar Arewa

Yemi Osinbajo ya yi magana kan yadda matasa za su kawo sauyi a Najeriya
Yemi Osinbajo ya ba matasan Najeriya shawarar shiga harkokin siyasa domin kawo sauyi. Hoto: @ProfOsinbajo
Asali: Twitter

Kungiyar EiE tare da BudgIT ne suka hada taron mai taken ‘Fasaha: Halin da ake ciki yanzu da makomar ayyukan siyasa a Afirka’ a cewar rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Tasirin kafofin sada zumunta' - Osinbajo

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya koka kan yadda matasa suka yi amfani da kafafen sada zumunta wajen shirya zanga-zanga a Najeriya, Kenya, da Zambia.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Osinbajo na cewa:

“Kafofin sadarwa suna ba kowa damar yin amfani da su, kuma suna ba kowa damar bayyana ra'ayinsa, ciki har da fadawa masu mulki gaskiya.
“Wadannan kafofi suna da amfani, amma dole ne mu nemo hanyoyin da za mu tsara yadda za a gudanar da su musamman a kasashen da ke samun ci gaba."

Hanyar kawo sauyi a kasashe masu ci gaba

Osinbanjo ya amince da cewa akwai lokutan da zanga-zanga ke da amfani, amma ya tabbatar cewa matasa za su iya kawo sauyi ne idan suka shiga harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan da ke yawan sukar gwamna a Najeriya

Ya jaddada cewa, dole matasa su shiga harkokin siyasa, domin su kawo wasu tsare tsare na warware matsalolin da ke hana ci gaban al'ummominsu.

Tsohon mataimakin shugaban ya ce shiga cikin harkokin siyasa na da muhimmanci don samun sauyi mai dorewa a kasashen da ke samun ci gaba.

Osinbajo ya magantu kan tsadar rayuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya nuna damuwa kan yadda tsadar rayuwa ta yi katutu a Najeriya.

Farfesa Osinbajo ya bukaci Gwamnatin Bola Tinubu da ta samar da hanyoyin inganta rayuwar al'umma duba da halin da matsin tattali da ake ciki a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.