Yanzu Yanzu: Osinbajo ya bukaci matasa dasu shiryawa jagorancin siyasa

Yanzu Yanzu: Osinbajo ya bukaci matasa dasu shiryawa jagorancin siyasa

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kalubalanci matasan Najeriya dasu shiryawa jagorancin siyasar kasar a shekaru masu zuwa

- Osinbajo ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matasa ta Not Too Young to Run a fadar shugaban kasa

- Osinbajo yace su shiryawa mukaman da sukeso su rike nan gaba saboda sammun wannan matsayi ba wai hakanan bane

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kalubalanci matasan Najeriya dasu shiryawa jagorancin siyasar kasar a shekaru masu zuwa.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matasa ta “Not Too Young to Run”, a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya.

Yanzu Yanzu: Osinbajo ya bukaci matasa dasu shiryawa jagorancin siyasa

Yanzu Yanzu: Osinbajo ya bukaci matasa dasu shiryawa jagorancin siyasa

Osinbajo yace su shiryawa mukaman da sukeso su rike nan gaba saboda sammun wannan matsayi ba wai hakanan bane, kamar yanda yace yana tinawa da lokacin da ya zama babban mai bayar da shawara kafin ya zama shima mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta daskarar da asusun bankin Fayose Yanzu Yanzu: Fusatattun sojoji sun kai ramuwar gayya inda suka cinnama wani kauye wuta a jihar Benue

Yace ya kasance yana shiga cikin al’amurran manyan kungiyoyi, yace duk da ya san abun ba sauki bane amma dai yana da kyau ace sun samu irin wannan horo, saboda Najeriya bata bukatar irin mutanen da ke dabaru su samu matsayi a kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel