'Ya Koma Sukar Gwamnati': 'Yan Sanda Sun Cafke Wani Tsohon Kwamishina a Najeriya

'Ya Koma Sukar Gwamnati': 'Yan Sanda Sun Cafke Wani Tsohon Kwamishina a Najeriya

  • Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa ita ce ta cafke Dakta Fabian Ihekweme, tsohon kwamishinan harkokin wajen Imo
  • Ta ce ta kama Ihekweme ne bayan ƙorafi daga wata ƙungiyar Imo, IDA, wacce ta zarge shi da ƙoƙarin haifar da tashin hankali
  • ‘Yan sanda sun musanta cewa 'yan bindiga ne suka sace Ihekweme, suna mai kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Rundunar ‘yan sandan Imo ta kama Dakta Fabian Ihekweme, tsohon kwamishinan harkokin wajen jihar, bisa zargin wallafa bayanai masu tayar da zaune tsaye.

An cafke Ihekweme, wanda yanzu ya zama dan adawa da gwamnatin Gwamna Hope Uzodimma bayan ƙorafi daga ƙungiyar Imo Democratic Alliance (IDA).

'Yan sanda sun yi magana bayan kama tsohon kwamishinan Imo
'Yan sanda sun cafke tsohon kwamishinan Imo saboda kalaman tunzurarwa. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

'Yan sanda cafke tsohon kwamishinan Imo

Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya ce an kama Ihekweme bayan samun takardar izinin kama shi, kan zargin tayar da fitina, inji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba: EFCC za ta sake gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okoye ya musanta rahotannin da ke cewa 'yan bindiga ne suka sace tsohon kwamishinan, yana mai kira ga jama’a su yi watsi da wannan labarin da ya kira "ƙarya".

“Mun lura da wasu rahotanni masu cewa wai an sace Dakta Ihekweme. Muna tabbatar muku cewa an kama shi ne bisa doka."

A cewar Henry Okoye.

"Dalilin cafke tsohon kwamishina" - 'Yan sanda

An kama Ihekweme a ranar 27 ga Nuwamba, 2024, bayan ƙorafi daga kungiyar IDA wanda ta zarge shi da wallafa bayanan da za su iya tayar da fitina.

Kungiyar ta yi zargin cewa kalaman da tsohon kwamishinan ke wallafawa a kan gwamnatin jihar na iya tayar da zaune tsaye a jihar, don haka akwai bukatar taka masa burki.

The Guardian ta rahoto rundunar ‘yan sandan jihar ta jaddada cewa tana aiki bisa doka ba tare da tsangwamar kowa ba.

'Yan bindiga sun sace tsohon kwamishina

Tun da fari, mun ruwaito cewa kafafen watsa labarai sun cika da labarin cewa 'yan bindiga ne suka kama tsohon kwamishinan Imo, Dakta Fabian Ihekweme.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan da ke yawan sukar gwamna a Najeriya

A wani faifan bidiyo da ya bazu a intanet, an ga wata mata da ta bayyana kanta a matsayin matar Ihekweme tana ikirarin wasu miyagu sun tafi da mijin nata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.