Kwanaki da Samun Mukami, Kawu Sumaila Ya Yabi Tinubu kan Abin Alheri a Kano
- Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya kora ruwan yabo ga shugaba Bola Tinubu kan abin alheri ga jihar Kano
- Sanatan Kano ta Kudu, Sumaila ya yaba shugaban kan saurin amincewa da N95bn domin inganta noman rani a yankin
- 'Dan majalisar ya ce wannan gudunmawa da shugaban ya bayar zai taimaka wurin bunkasa harkokin noma a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sanata Kawu Sumaila ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan amincewa da aikin noman rani a jihar Kano.
Sanata Kawu Sumaila da ke wakiltar Kano ta Kudu ya ce Tinubu ya amince da ba da N95bn domin bunkasa noman rani a mazabarsa.
Sanata Kawu Sumaila ya yabi Tinubu kan noma rani
Daily Nigerian ta ce Sumaila ya fadi haka ne yayin ba da gudunmawa kan kirkirar Jami'ar Kura a Kano a zaman Majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya yabawa Tinubu kan amincewa da aikin inda ya ce hakan zai bunkasa harkokin noma a fadin jihar.
Sumaila ya ce mazauna yankin sun shafe akalla shekaru 30 rabonsu da samun wannan tallafi.
Sumaila ya fadi soyayyar Tinubu ga yan Najeriya
"Bayan na nemi alfarma a madadin mutanen Kano ta Kudu, mai girma shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da bukatarmu domin gyara da cigaba da kula da shirin noman rani a Kano."
"Cikin hikima da kuma soyayyarsa ga yan Najeriya, Tinubu ya amince da ba da N95bn gare mu."
"A cikin shekaru 50, ba a taba samun irin wannan ba, babu wani abu makamancin haka da za aka ce an ci moriya."
- Kawu Sumaila
Sanatan ya ce an kammala 90% na aikin yayin da ya ce nan ba da jimawa ba 'yan kwangila za su tabbatar an fara amfanin da dam da harkokin noman rani.
Majalisar Dattawa ta ba Sanata Sumaila mukami
Kun ji cewa Sanata Kawu Sumaila daga jihar Kano ya samu mukamin shugaban kwamitin albarkatun mai a Majalisar Dattawa.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio shi ya nada Sumaila domin maye gurbin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah da ya rasu.
Wannan nadin ya jawo maganganu duba da Sumaila dan NNPP ne kuma wasu na ganin dan Kudu ya kamata a nada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng