Tinubu Ya Sakawa Ɗan MKO Abiola, Ya Gwangwaje Shi da Mukami a Gwamnatinsa
- Shugaba Bola Tinubu ya nada ɗan marigayi Moshood Abiola (MKO) muƙamin hadiminsa na musamman a gwamnatinsa
- Tinubu ya nada Jami'u Abiola a matsayin hadimi a bangaren yarurruka da harkokin kasashen waje
- Kafin nadin Jami'u wannan mukami ya rike hadimi a ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake nada hadimi na musamman a gwamnatinsa.
Tinubu ya nada ɗan MKO Abiola mai suna Jami'u Abiola hadimi a bangaren yarurruka da harkokin kasashen waje.
Tinubu ya nada dan MKO Abiola muƙami
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 27 ga watan Nuwambar 2024, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cif Moshood Abiola (MKO) ya yi nasara a zaben watan Yunin 1993 da aka rusa a mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Har ila yau, an bindige matarsa marigayiya Kudirar Abiola yayin da take gwagwarmaya domin neman hakkin mijinta da aka rusa zabensa.
A cewar sanarwar, muƙamin ya fara aiki ne tun a ranar 14 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki domin inganta harkokin gwamnati.
Muƙamin da Jami'u ya riƙe a baya
Kafin wannan nadi, Jami'u ya rike muƙamin hadimi a bangaren ayyuka na musamman a ofishin mataimakin shugaban kasa.
Tinubu ya bukaci Jami'u ya yi haɗaka da ma'aikatar harkokin kasashen waje tare da kwarewarsa wurin kawo sauyi a kasa, cewar Vanguard.
"Muƙamin Jami'u ya fara aiki ne tun a ranar 14 ga watan Nuwambar 2024 wanda ya yi daidai da tsarin dokar rike ofis na siyasa da bangaren Shari'a."
- Cewar sanarwar
Tinubu ya nada Bwala muƙami a gwamnati
A baya, mun baku labarin cewa Bayan dogon jira, Daniel Bwala ya samu muƙami a gwamnatin Bola Tinubu a yau Alhamis 14 ga watan Nuwambar 2024.
Shugaba Tinubu ya amince da nadin Bwala a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren sadarwa da hulda da jama'a.
Wannan na zuwa ne bayan shafe watanni Bwala na yabon gwamnatin Tinubu, bayan ya yi watsi da Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng