Kudirat Abiola: Al-Mustapha zai fasa kwai

Kudirat Abiola: Al-Mustapha zai fasa kwai

– Dogarin tsohon shugaban kasa Janar Abacha zai fasa kwai

– Hamzah Al-Mustapha yace yana shaida game da kisan Matar Abiola

– An zargi Al-Mustapha da laifin kashe Kudirat Abiola

Kudirat Abiola: Al-Mustapha zai fasa kwai
Kudirat Abiola: Al-Mustapha zai fasa kwai

Manjo Hamzah Al-Mustapha mai ritaya Dogarin tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha yace zai fasa kwai har idan fa ta kama a game da shari’ar kisan Uwargidan tsohon dan takarar shugaban kasa Marigayi Mashood Abiola.

An zargi Manjo Hamzah Al-Mustapha da laifin kashe matar MKO Abiola a shekarun baya. Manjon mai ritaya yace yana da wasu takardu wanda idan har ya nuna su a gaban Kotu idan har dalili ya sa hakan zai mika su.

KU KARANTA: Matan tsofaffin shugaban kasa

Al-Mustapha ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi da Gidan Talabijin na 360. Tsohon Dogarin yace akwai wata wasika da za ta wanke shi idan an nemi a zauna a Kotu. Al-Mustapha yace wasu ne dai ke kokarin ganin bayan sat un mutuwar mai gidan sa Janar Abacha.

Yanzu haka kuma dai shugaba Buhari ya fasa dawowa daga hutun da ya tafi, ya kuma bayyana dalilan sa na yin hakan. Shugaban kasa Buhari ya bayyana hakane a wata wasika da ya turawa Majalisar Kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel