Abba Ka Cika Gwarzo: Ma'aikata Sun Yabawa Gwamnan Kano bayan Dafe Sabon Albashi

Abba Ka Cika Gwarzo: Ma'aikata Sun Yabawa Gwamnan Kano bayan Dafe Sabon Albashi

  • Kungiyoyin 'yan kwadago a Kano sun yabawa yadda gwamnati ta fara biyan ma'aikata mafi karancin albashi
  • Makonni uku da su gabata ne gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki alkawarin biyan ma'aikata mafi karancin albashi
  • Kungiyoyin NLC da NMA sun bayyana gamsuwa da yadda gwamnati ta damu da rayuwar ma'aikata a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Ma'aikatan gwamnatin Kano sun fara sam barka bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin da ya dauka kan karin lbashi.

A ranar Talata ne ma'aikata da dama su ka bayyana ganin karin albashi domin daidaitawa da dokar mafi karancin albashin N70,000

Kabir
Ma'aikata sun yaba wa gwamnan Kano bayan fara biyan mafi karancin albashi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa kungiyar kwadago ta NLC, reshen Kano ta yaba da yadda gwamnatin jihar ta fara tabbatar da biyan N71,000 ga ma'aikata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya cika alkawari, ma'aikata sun fara cin sabon albashin N71,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan Kano sun ji dadin karin albashi

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ma'aikatan lafiya karkashin kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta jinjinawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa biyan mafi karancin albashi.

Jami'in hulda da jama'a na kungiyar, Dr. Mohammed Aminu Musa ya ce gwamnati ta kara albashin likitoci da ke tsarin albashi na CONMESS.

Kano: NLC ta fadi amfanin karin albashi

Shugaban NLC na Kano, Kwamred Kabiru Inuwa ya ce gyaran albashin da gwamnatin Kano ta dabbaka zai inganta rayuwar ma'aikata.

Kwamred Kabiru Inuwa ya ce;

"Muna amfani da wannan dama wajen yabawa gwamnan da ya damu da ma'aikata da yan fasho, saboda yadda ya sanya bukatar ma'aikata a gaba ta hanyar nuna jajircewa a wannan lokaci mai cike da kalubale."

Gwamnan Kano ya cika alkawarin karin albashi

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta cika alkawarin biyan ma'aikata mafi karancin albashin N71,000 bayan gwamnatin tarayya ta yi umarnin a rika biyan akalla N70,000.

Kara karanta wannan

Duba marasa lafiya kyauta ya tsokano bala'i, an kwantar da daruruwan mutane a asibiti

Shugaban ma'aikatan Kano, Alhaji Abdullahi Musa ya tabbatar cewa ma'aikata sun fara ganin karin albashin mako uku bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a yi karin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.