An Shiga Firgici a Kaduna, Ƴan Bindiga Sun Sace Yaro Ɗan Shekara 2 da Wasu Mata 3

An Shiga Firgici a Kaduna, Ƴan Bindiga Sun Sace Yaro Ɗan Shekara 2 da Wasu Mata 3

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani yaro dan shekara biyu da wasu 'yan uwansa mata uku
  • Mahaifin yaran, Yunusa Sarkin Samarin Keke ya bayyana cewa ya ziyarci matarsa da ke asibiti a lokacin da aka sace yaran
  • Yunusa ya ce an samu takalman yaran a watse a kofar gida, kuma gidansa ne kadai masu garkuwan suka farmaka a ranar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - An shiga firgici a garin Keke A da ke Millennium City, jihar Kaduna, bayan sace wani yaro mai shekaru biyu da wasu ‘yan uwansa mata uku.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe tara na daren Talata, yayin da mahaifinsu ya ziyarci mahaifiyarsu a asibiti.

Magidanci ya koka yayin da masu garkuwa suka sace 'ya'yansa hudu a Kaduna
Ana fargabar 'yan bindiga sun yi garkuwa da kananan yara hudu a jihar Kaduna. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An sace yara 4 a jihar Kaduna

Kara karanta wannan

'Kun jefa mu a talauci': Malamin addini a Sokoto ya caccaki ƴan siyasar Najeriya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda aka sace sun hada da yaro mai shekaru biyu, da ‘yan mata uku masu shekaru tara, 12 da 15, lamarin da ya firgita al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifin yaran, Yunusa Sarkin Samarin Keke, ya bayyana cewa daya daga cikin yaran maraya ne da yake kula da shi.

“Na je duba matata a asibiti lokacin da abin ya faru. Na dawo gida na tarar dukkansu an tafi da su."

- A cewar Yunusa.

Yadda ake zargin 'yan bindiga sun sace yaran

Yunusa ya ce yana zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace yaran saboda an samu takalman yaran a watse a kofar gida, kuma gidansa kadai aka kai wa harin.

Mazauna yankin sun yi zargin cewa masu satar sun haura ta katanga ne don kada a gansu, kasancewar mutane suna cikin gidajensu lokacin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu Bayan Tinubu Ya Kore Ta

An rahoto cewa Yankunan Keke da Millennium City da ke jihar Kaduna na ci gaba da fuskantar ayyukan masu garkuwa da mutane.

Jaridar ta ce ta kasa samun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan, domin jin ta bakinsa game da lamarin.

'Yan bindiga sun sace malami a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addinin musulunci da iyalinsa da kuma sababbin ma'aurata a Kaduna.

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce lamarin ya faru ne a yankin Dan-Honu da ke Millennium City, karamar hukumar Chikun da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.