An Saki Bama Bamai kan Tarin Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari ga Sojoji

An Saki Bama Bamai kan Tarin Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari ga Sojoji

  • Rahotanni na nuni da cewa rundunar sojin saman Nigeriya ta kai jerin hare hare kan yan ta'addar Boko Haram a wasu yankunan jihar Borno
  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka da dama daga cikin yan ta'addar tare da abubuwan hawa da suka zo da su domin kai hari ga jami'an tsaro
  • Rundunar sojin saman Najeriya ta ce za ta cigaba da haɗa kai da sojojin kasa domin hana yan ta'adda samun sukuni a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan tarin yan ta'addar Boko Haram a yankin Kukawa na jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe yan ta'adda da dama yayin da wasu suka gudu bayan samun munanan raunuka.

Sojoji
Sojojin sama sun kai kan Boko Haram. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa yan ta'addar sun taru ne domin kai hari ga sojojin ƙasa kafin a saki wuta a kansu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi gaba da gaba da yan ta'adda, an kashe miyagu da dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun saki bam kan yan ta'adda

Rahotanni da suka fito daga jihar Borno na nuni da cewa an fafata tsakanin sojojin Najeriya da yan ta'addar Boko Haram.

Kakakin sojojin saman Najeriya, Olusola Akinboyewa ya bayyana cewa sun lalata kayayyakin yan ta'addar da dama yayin fadan.

Olusola Akinboyewa ya kara da cewa sojojin saman sun samu kiran gaggawa ne daga sojojin ƙasa a lokacin da suke gumurzu da yan Boko Haram.

"A karon farko, jirgin sojojin sama ya lalata motar bindigar yan ta'addar da kashe wasu da dama a cikinsu.
Bayan sakin wuta a karo na biyu, yan ta'addar sun gudu sun bar babura sama da 20 kuma an kashe wasu masu yawa a cikinsu."

- Olusola Akinboyewa

A yanzu haka dai sojojin kasan Najeriya sun bi sawun yan ta'addar da suka gudu da raunuka domin karasa hallaka su.

Leadership ta wallafa cewa Olusola Akinboyewa ya ce nasarar da sojojin suka samu alama ce da ke nuna Najeriya na cin galaba kan yan ta'adda.

Kara karanta wannan

An kama yan ta'adda da miyagu 523, an ceto mutane 102 a Kaduna

Sojoji sun budewa Boko Haram wuta

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar hallaka mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Rahotanni na nuni da cewa sojojin Najeriya sun saki wuta kan Boko Haram ne yayin da miyagun suke tsaka da wata tattaunawa a daji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng