An Kama Matasan Gari da ke Taimakon Yan Bindiga da Bayanai a Daji
- Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta kama wasu mutane da ake zargi da cewa suna hada kai da yan bindiga wajen garkuwa da mutane
- Ana zargi matasan da tara bayanan mutanen da ke zaune a gari musamman baƙi su mika ga miyagu domin a yi garkuwa da su saboda kudi
- 'Yan sanda sun bayyana cewa matasan sun hada baki da yan bindiga a lokuta mabanbanta wajen satar mutane da karbar kudin fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - 'Yan sanda sun kama wasu matasa biyu da ake zargi suna hada baki da masu garkuwa da mutane.
'Yan sanda da ke bangaren yaki da garkuwa da mutane ne suka kama miyagun a karamar hukumar Alkaleri.
Rundunar yan sandan Bauchi ta wallafa a Facebook cewa matasan na bayar da bayanan sirri kan yadda za a yi garkuwa da mutane a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama masu taimakon yan bindiga
A ranar 10 ga Nuwamba 2024, 'yan sanda suka kama wasu matasa da ake zargi da taimakon masu garkuwa da mutane.
Ana zargin cewa matasan suna duba mutane masu hannu da shuni suna sanar da yan bindiga domin a yi garkuwa da su.
"A ranar 7 ga Satumba sun taimaka an yi garkuwa a ƙauyen Garin Gambo, aka karbi kudin fansa N4m.
Haka zalika sun taimaka an yi garkuwa a ƙauyen Gub inda aka karbi kudin fansa N3m.
Ana zargin matasan sun taimaki yan bindiga wajen kama mutane uku a unguwar Gero, aka karbi N14m kuma aka kashe mutane biyu da aka sace."
- Rundunar yan sanda
Daya daga cikin matasan mai suna Yusuf ya bayyana cewa ba wani kudi sosai ake ba su ba, ya ce an taba ba shi N10,000 da N3,000.
Kakakin yan sanda, SP Ahmed Mohammed Wakili ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an gama bincike.
Hukuma ta kama dan damfara a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani dan damfara a Kano mai karyar cewa shi kanin Sheikh Abdallah Gadon Kaya ne.
Mutumin mai suna Aminu Abdullahi ya shiga hannun yan sanda ne bayan ya yi damfara a jihar Kano kuma mutane sama da 20 sun ce ya cuce su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng