IPMAN: 'Yan Kasuwa Sun Fadi Abin da Zai Kawo Cikas ga Samun Saukin Farashin Fetur

IPMAN: 'Yan Kasuwa Sun Fadi Abin da Zai Kawo Cikas ga Samun Saukin Farashin Fetur

  • Dillalan man fetur na kungiyar IPMAN ta na ganin matatar Fatakwal da aka gyara za ta kawo saukin da aka sa rai ba
  • Sakataren kudi na kungiyar, Musa Yahaya Mai Kifi ya tabbatarwa da Legit cewa amma hakan ba ya nufin ba za a samu sauki ba
  • Ya tabbatar da cewa akwai wata sahihiyar hanya da gwamnatin Najeriya za ta iya bi wajen tabbatar da an samu sauki sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa gyaran matatar mai ta Fatakwal ba za ta samar da saukin da ake fata ba.

Sakataren kudi na kungiyar, Musa Yahaya Mai Kifi ne ya tabbartwa Legit da haka yayin da ya ke bayanin yadda gyaran matatar Fatakwal zai kawo saukin farashi.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya nemo hanyar yakar Lakurawa, ya fadi masu daukar nauyinsu

IPMAN
IPMAN ta yi madallah da gyara matatar Fatakwal Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Musa Yahaya Mai Kifi ya jaddada cewa amma wananna ba ya nufin ba za a samu saukin farashin fetur a gidajen mai ba, domin ko a yanzu an samu sauki da matatar Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar IPMAN ta fadi dalilin tsadar man fetur

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), ta bayyana abin da ke jawo tsadar farashin man fetur a kasar nan.

Sakataren kudi na kungiyar, Musa Yahaya Mai Kifi ya ce;

“Dokar ita ce duk wanda aka tono (danyen mai), za a sayar da shi a kan farashin kasuwar duniya, a farashin duniya kuma kin ga maganar farashin Dala ake yi, Dalan nan kuma ga yanayin yadda tsadarta ta ke.”

IPMAN ta ba da shawara domin a ga saukin fetur

Musa Yahaya Mai Kifi ya ce akwai hanyar da gwamnati za ta bi matukar ta na da bukatar sauko da farashin litar fetur.

Sai dai in har majalisa za ya iya kiran dokar ta yi mata gyara, ya zamanto duk man da za a sayar a waje, ya tafi a farashin duniya. Wanda kuma za mu sha a gida ya zamanto shi an ba shi wata kulawa ta musamman.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi adadin fetur da matatar Fatakwal za ta samar a kullum

IPMAN ta cimma yarjejeniyar fetur da Dangote

A baya kun ji cewa kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta samu nasarar kulla yarjejeniya da matatar Dangote domin samar da lita akalla miliyan 240 na fetur a kowane wata.

Matatar ta amince da ba IPMAN fetur bayan an jima ana kokari kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya amincewa ''yan kasuwa su rika dakon tataccen fetur kai tsaye ba tare da katsalandan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.