Wata Matsala Ta Taso, Dangode Zai Bayyana gaban Majalisa domin Amsa Tambayoyi

Wata Matsala Ta Taso, Dangode Zai Bayyana gaban Majalisa domin Amsa Tambayoyi

  • Majalisar dokokin Ogun ta gayyaci kamfanin Dangote ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi da suka shafi ayyukansa
  • Majalisar ta gayyaci Dangote ne bayan korafe korafe daga jama'ar yankin Ibese inda dan kasuwar ya gina kamfanin simintinsa
  • Ana zargin kamfanin simintin Dangote na cin zarafin muhalli, rashin mutunta jin dadin mazauna yankin da saba wasu ka'idoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Majalisar dokokin jihar Ogun ta cimma matsaya a ranar Talata ta gayyatar shugabannin kamfanin simintin Dangote domin amsa tambayoyi.

Majalisar na so Dangote ya gabatar da tsarin ginin kamfaninsa na Ibese, ciki har da wurin ajiye manyan motoci da magudanun ruwa na masana'antar.

Majalisar jihar Ogun ta yi bayani yayin ta cimma matsayar gayyatar Dangote
Majalisar Ogun ta gayyaci Dangote kan zargin cin zarafin muhalli da sauransu. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Majalisar Ogun ta nemi ganin Dangote

Matakin ya biyo bayan rahoton da kwamitocin hadin gwiwa na kasuwanci, zuba jari da muhalli suka gabatar, karkashin jagorancin Adebisi Oyedele, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bayan auren 'Yar Kwankwaso da Dan Mangal, gwamnati ta rufe ofishin jirgin Max Air a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Oyedele ya ce an samu kamfanin Dangote da laifin watsi da jin dadin al'ummar da ke makotaka da kamfanin duk da shafe tsawon shekaru yana aiki a wajen.

Dan majalisar ya bayyana yadda rashin samar da garejin tirela, magudanun ruwa ya jefa mutane cikin wahala tsawon shekaru ba tare da kamfanin ya damu ba.

Abubuwan da ake so Dangote ya yi

Majalisar Ogun ta bukaci cikakken tsari daga Dangote na yadda zai magance lalacewar muhalli da kawo karshen ajiye motocin da ake yi ba bisa tsari ba.

Kwamitin ya bada shawarar cewa kamfanin Dangote ya gabatar da taswirar da aka gina cibiyar a kai, sannan ya amsa tambayoyin da ake yi kan ingancin tsarin aikinsa.

Majalisar ta ce akwai bukatar Dangote ya inganta ayyukansa na jin dadin al'umma tare da daukar matakai kan korafe-korafen da ake yi kan kamfaninsa.

Majalisa za ta gana da Dangote, BUA

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya fadi shugabannin da suka fi gwamnoni kwarewa a karbar rashawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta gayyaci Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu (BUA) da sauran masu kamfanonin siminti a Najeriya.

Hon. Gaza Jonathan Gbefwi, da Hon. Ademorin Kuye ne suka gabatar da bukatar gayyatar kamfanonin sakamakon tsadar simintin da ake fama da shi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.