Kano da Wasu Jihohi 23 da Za Su Amfana da Bashin $500m da Tinubu Ya Karbo
- Akalla jihohi 25 za su amfana da sabon lamunin $500m daga Bankin Duniya domin inganta albarkatun ruwa da makamshi
- Jihohin da za su amfana da wannan rance sun hada da Benuwai, Katsina, Akwa Ibom, Neja, Gombe, Sokoto, Enugu da sauransu
- Lamunin zai inganta tsaron dam, gudanar da albarkatun ruwa da kuma haɓaka tsarin wutar lantarki da noman rani a ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kimanin jihohi 25 ne za su amfana da sabon rancen $500m daga Bankin Duniya domin inganta albarkatun ruwa ta fuskar noman rani da samar da lantarki.
Gwamnatin Tarayya, ta hannun ma’aikatar albarkatun tuwa da ma’aikatar wutar Lantarki, ta sanya hannu kan yarjejeniyar tare da Bankin Duniya.
Za a bunkasa albarkatun ruwa a jihohi
Jaridar Punch ta ce an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata domin aiwatar da shirin "Dorewar wuta da noman rani a Najeriya" wanda zai inganta albarkatun ruwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron sanya hannun ya samu halartar ministan albarkatun ruwa da tsabtace muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da ministan makamashi, Adebayo Adelabu.
An bayyana wannan ci gaba ne a cikin wata sanarwa da Bolaji Tunji, mai ba da shawara na musamman ga ministan makamshi ya fitar.
Jihohin da za su amfana da lamunin
- Benuwai
- Katsina
- Akwa Ibom
- Neja
- Gombe
- Sokoto
- Enugu
- Bauchi
- Cross River
- Nasarawa
- Ekiti
- Kebbi
- Filato
- Ebonyi
- Zamfara
- Abia
- Kwara
- Imo
- Taraba
- Kano
- Delta
- Osun
- Jigawa
- Edo
- Kogi
Sanarwar ta ce shirin zai inganta tsaron madatsun ruwa, gudanar da albarkatun ruwa da kuma haɓaka tsarin wutar lantarki da noman rani a fadin ƙasar, inji rahoton Guardian.
A jawabin Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya jaddada mahimmancin hadin gwiwa wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma inganta tsaron makamashin Najeriya.
Bankin Duniya ya ba Najeriya rancen $500m
Tun da fari, mun ruwaito cewa kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da cewa Bankin Duniya ya ba Najeriya lamunin dala miliyan 500.
Kamfanin TCN ya ce sabon lamunin zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen inganta ayyukan kowanne kamfani na rarraba wutar lantarki a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng