'Kun Jefa Mu a Talauci': Malamin Addini a Sokoto Ya Caccaki Ƴan Siyasar Najeriya

'Kun Jefa Mu a Talauci': Malamin Addini a Sokoto Ya Caccaki Ƴan Siyasar Najeriya

  • Bishop Mathew Kukah ya bayyana damuwa game da rashin ingantaccen ilimi a Arewacin Najeriya, ya ce laifin 'yan siyasa ne
  • Malamin addinin da ke zaune a Sokoto ya tuna yadda Sir Ahmadu Bello ya gabatar da ilimin bai-daya a Arewa domin yaki da jahilci
  • Bishop Kukah ya nuna muhimmancin saka mata a cikin shirin zaman lafiya da tsaro yayin da ya ce 'yan siyasa sun kawo talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Malamin addini a Sokoto, Bishop Mathew Kukah ya bayyana damuwa game da rashin ingancin ilimi a Arewa, yana mai dora laifin ga 'yan siyasa.

Bishop Kukah Ya yi magana ne a taron tattaunawa kan shigar mata cikin shirin zaman lafiya da tsaro, wanda Global Right da gidauniyar Kukah suka shirya.

Kara karanta wannan

'Ya manta asalinsa': Dan majalisar LP ya shan suka saboda sanya 'hular Tinubu'

Malamin addini a Sokoto ya yi magana kan rashin ilimi a Arewa da alakarsa ga 'yan siyasa
Mathew Kukah ya yi ikirarin cewa 'yan siyasa sun jefa jama'a a cikin talauci. Hoto: @Ekwulu
Asali: Twitter

Kukah ya tuno yadda Sir Ahmadu Bello ya gabatar da ilimin bai daya a Arewa domin yaki da jahilci da kuma inganta ilimi a shiyyar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin kirista ya caccaki 'yan siyasa

Malamin ya yi suka ga 'yan siyasa, wadanda ya ce suna karban kuri'un mutane amma suna jefa jama'a cikin talauci maimakon ba su ilimi.

"Lokacin da Sardauna ya ga ci gaban Kudu, ya kaddamar da shirin yaki da jahilci domin tabbatar da cewa mutanen Arewa suna iya karatu da rubutu.
"Amma 'yan siyasar mu na yanzu suna karbar kuri'unmu, ba ilimi suke ba mu ba, sai dai su jefamu a talauci."

- A cewar Bishop Kukah.

Bishop Kukah ya nuna muhimmancin mata

Babban faston ya jaddada cewa babu wani abu da zai iya maye gurbin ilimi, inda ya yi gargadin cewa jahilci yana haifar da talauci da dakile ci gaba.

Kara karanta wannan

NNPP da APC: Yadda yan siyasa ke wasa da masarautar Kano

Bishop Kukah ya ce idan har aka ba mata dama, to za su taka rawa sosai wajen magance wasu daga cikin matsalolin da ake fuskanta, musamman a ilimi.

Kalaman Bishop Kukah suna nuni ne da muhimmancin mata wajen samar da tsaro da zaman lafiya, yana mai yin kira ga 'yan kasar da su hada kansu domin samun ci gaba.

Kukah ya fadawa jiga jigan APC gaskiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa malamin addini a Sokoto, Bishop Mathew Kukah ya tsagewa jiga jigan jam'iyyar APC gaskiya kan halin yunwa da ake ciki a kasar.

Bishop Kukah ya ce 'yan Najeriya na fama da tsadar rayuwa a karkashin gwamnatin APC don haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta rage kudin man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.