Sojoji Sun yi gaba da gaba da Yan Ta'adda, An Kashe Miyagu da dama
- Rundunar sojin Najeriya ta yi arangama da yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo kuma sojojin Najeriya sun kashe da dama daga cikin yan ta'addar yayin fafatawar
- Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta kwato da dama daga cikin makaman da yan ta'addar ke amfani da su yayin faɗan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo - An fafata a wani kazamin fada tsakanin sojojin Najeriya da yan ta'addar IPOB a Kudu maso Gabas.
A ranar Litinin dakarun rundunar sojin Najeriya suka yi gaba da gaba da yan ta'addar IPOB a karamar hukumar Orsu.
Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kashe yan ta'addar IPOB
Dakarun rundunar sojin Najeriya a karkashin Operation Udo Ka sun ragargaji yan ta'addar IPOB a jihar Imo.
Sojojin Najeriya sun kashe yan ta'addar IPOB da dama a kokarin kakkaɓe miyagun a yankin Kudu maso Gabas baki daya.
Bayan kashe wasu daga cikin yan ta'addar, dakarun sojin sun kwato makamai da miyagun ke aiki da su wajen ta'addanci.
"Sojoji sun fafata da yan ta'addar IPOB da ESN. Yayin da aka kara, an kashe wasu da ake zargi yan ta'adda ne.
Daga cikin abubuwan da aka kama a wajensu akwai bindigogi, abubuwa masu fashewa da kayayyakin tsafi."
- Rundunar sojin Najeriya
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa mukaddashin shugaban sojojin Najeriya ya yabawa dakarun bisa kokarin da suka yi.
Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya yi kira ga mutanen yankin da su cigaba da harkokinsu na yau da kullum.
An kama yan ta'adda a Kaduna
A wani rahoton, mun labarta muku cewa rundunar yan sanda a Kaduna ta fitar da rahoto kan nasarar da ta samu a watanni biyu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna ya bayyana cewa sun kama masu manyan laifuffuka sama da 500 da kuma ceto mutane sama da 100 a hannun masu garkuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng