An Kama Yan Ta'adda da Miyagu 523, an Ceto Mutane 102 a Kaduna
- Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta yi nasarar kama tarin miyagu da suka aikata laifuffuka daban daban a fadin jihar
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama yan ta'adda da sauran bata gari 523 da suka hada da masu garkuwa da mutane
- Haka zalika rundunar yan sandan ta samu nasarar ceto mutane 102 daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Yan sandan Najeriya a jihar Kaduna sun yi holon mutanen da suka kama daga Okotoba zuwa Nuwamba.
Haka zalika rundunar yan sandan ta ce ta samu nasarar ceto jama'a daga hannun masu garkuwa da mutane.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamishinan yan sanda, CP Ibrahim Abdullahi ne ya fitar da sanarwar a yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama miyagu 523 a Kaduna
CP Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da cewa daga watan Oktoba zuwa Nuwamba sun kama tarin miyagu har 523.
Tun ranar 21 ga Oktoba CP Ibrahim Abdullahi ya fara aiki a jihar Kaduna kuma ya mayar da hankali a kan kama masu laifi da hada kan jami'an tsaro.
The Sun ta wallafa cewa CP Abdullahi ya ce dabarun da suka fara ne suka taimaka musu wajen kama miyagun
Laifuffukan da miyagu 523 suka aikata
Yan sanda sun bayyana cewa an kama miyagun ne da laifuffukan da suka hada da garkuwa da mutane.
Haka zalika ana zargin miyagun da satar motoci, satar wayoyin hannu da sauran laifuffuka. Ga adadin wasu masu laifi da abin da ake zarginsu da yi:
- Masu garkuwa 26
- Barayin shanu 12
- Barayin waya 97
- Barayin mota 17
- Masu fyade 10
An ceto mutane 102 a Kaduna
Bayan kama miyagun, yan sanda sun ceto rayuka kimanin 102 daga hannun masu garkuwa da mutane.
Haka zalika an kwato bindigogi kirar AK47 guda biyar, Pistol daya, shanu 283, tumaki 20 da tarin harsashi.
An kama barawo a masallacin Juma'a
A wani rahoton, kun ji cewa an kama barawon da ya shahara da sata a masallacin Juma'a a jihar Kano.
Jami'an NSCDC sun cafke barawon bayan ya sato kayan sola a masallacin Juma'a na unguwar Dakata yana ƙoƙarin sayar da su.
Asali: Legit.ng