Yadda ‘Aljan’ ya kwato daruruwan shanu, bindigu daga barayin shanu a jahar Kaduna

Yadda ‘Aljan’ ya kwato daruruwan shanu, bindigu daga barayin shanu a jahar Kaduna

Wani jarumi daya shahara wajen kama barayi da miyagu a jahar Kaduna, Shehu Musa Aljan ya sake samun nasara yayin da yayi arangama da wasu gungun yan bindiga da suka tattara shanun mutane da nufin haurawa dasu gadar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito barayin sun sato dabbobin ne daga kauyen Rijana dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi kokarin tserewa dasu ta kan gadar rafin Kaduna, amma suka ci karo da Aljan.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Buhari zai gina sabuwar jami’ar rundunar Sojan sama a Bauchi

Yadda ‘Aljan’ ya kwato daruruwan shanu, bindigu daga barayin shanu a jahar Kaduna
Aljan
Asali: Facebook

A dalilin wannan kicibus da suka yi da Aljan, barayin sun yi asarar dabbobinsu gaba daya, bindgunsu guda biyu kirar AK 47, sa’annan Aljan ya samu nasarar kama wani kasurgumin barawo daga cikinsu.

A zantawar da Aljan ya yi da majiyarmu ya bayyana yadda lamarin ya auku kamar haka: “Ina gida na samu labarin an sace wasu shanu daga Rijana kuma an hangesu a daidai gadar tafkin Kaduna, don haka na tafi fa kaina domin sa ido a hanyar da zasu bi.

“Cikin dare sai wasu mutane suka sameni wai sun samu labarin ina kan hanyar, don haka zasu bani naira miliyan 2 domin na kyalesu su wuce da shanun da suka sato. Ni kuma na biye musu, nan take suka ajiye min N856,000 da alkawarin zasu cika min kudina idan sun haura da shanun.

“Ganin haka yasa na kama barawon da suka aiko min, koda muka isa inda suke jiran komawarsa sauran sun tsere tare da bindigunsu, amma sun saki shanun.” Inji shi.

Game da batun sulhu da yan bindiga kuwa, Aljan ya nuna rashin amincewarsa da matakin, inda yace yan bindiga ba abin yarda bane, saboda idan har da gaske suke toh su fara mika dukkanin makamansu sa’annan su saki duk mutanen dake hannunsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng