Tattalin Arzikin Najeriya Ya Fara Farfadowa, NBS Ta Bayyana Cigaban da Aka Samu
- Tattalin arzikin Najeriya (GDP) ya karu da kashi 3.46% a zango na uku na 2024, wanda ya fi zarce 2.54% da aka samu a 2023
- Bangaren ayyuka ya karu da kashi 5.19%, wanda ya bayar da gudunmawar 53.58% ga habakar tattalin arzikin kasar a bana
- Sashen da ba na mai ba, ciki har da noma da sadarwa, gidaje da ciniki sun bayar da gudunmawa a farfadowar tattalin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tattalin arzikin Najeriya, a ma'aunin GDP ya karu da 3.46% a zango na uku na shekarar 2024, fiye da 2.54% da aka samu a zango na uku na 2023.
Rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa bangaren ayyuka shi ne ya fi jawo karuwar tattalin arzikin, inda ya samu habakar 5.19%.
Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 3.46%
Rahoton NTA News ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya a farashin kayayyaki yana a matsayin Naira tiriliyan 20.12, wanda ya zarce Naira tiriliyan 19.44 da aka samu a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shi kuwa tattalin arzikin kasar a ma'aunin ayyuka da kayayyakin da aka hada a kasar ya karu zuwa Naira tiriliyan 71.13, kimanin kaso 17 a mizanin shekara-shekara.
Bangarorin da suka samar da karuwar tattalin arzikin a ma'aunin ayyuka da kayayyaki su ne noma (26.51), kasuwanci (14.78%), sadarwa (13.94), mai (5.57%) da gidaje (5.43%).
Yadda kowane fanni ya cigaba a 2024
A habakar manyan bangarorin tattalin ariziki, darajar noma ta karu da 14%, masana'antu da 2.18%, yayin da ayyuka suka karu da 5.19%, inji rahoton Channels TV.
Noma ya bayar da gudunmawar 28.65%, masana'antu 17.77%, sai ayyuka 53.58%, sai sashen ayyuka ya samu mafi girman cigaba na mizanin shekara-shekara.
Bangaren mai ya karu da 5.17%, inda ya bayar da gudunmawar kashi 5.57% ga habakar GDP, tare da samar da ganga miliyan 1.4 a kowace rana.
Sashen da ba na mai ba ya bayar da gudunmawar 94.43%, wanda aka samu daga noma, ciniki, sadarwa da Gidaje.
Nasarorin Tinubu a gyaran tattalin arziki
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu na samun gagarumar nasara a gyaran tattalin arziki kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.
Nasarorin da Tinubu ya samu kan tattalin arziki sun hada da samun rarar ciniki, daina shigo da mai, karuwar kudin ajiyar waje, da dai sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng