Tattalin arzikin Najeriya ya habaka a zango na uku a bana - Hukumar Kididdiga ta Kasa
Hukumar Kididdiga na Kasa (NBS) ta fitar da rahoton tattalin arzikin Najeriya na zango na uku na 2018, alkalluman da hukumar ta fitar ya nuna cewa an samu karuwar hada-hada inda aka samu kari na 1.8% wanda ya dara 1.5 da aka samu a zango na biyu a kasar.
Rahoton da hukumar kididdiga na kasa NBS ta fitar na zango uku ne shekarar 2018 a ranar Litinin ya nuna cewa an samu karuwar arziki da 1.8% a wannan shekarar.
Rahoton da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo ya ce karin na 1.8% ya nuna cewa an samu cigaba idan aka kwatanta da karin 1.5% da tattalin arzikin Najeriya ya samu a zango na biyu na shekarar 2018 kamar yadda Punch ta ruwaito.
DUBA WANNAN: 2019: Korafin babban sarki a arewa ya kai APC hannun DSS
Idan aka sauya karin zuwa tsabar kudi, rahoton ya nuna cewa anyi hada-hadar kudade har Naira tiriliyan 33 wanda ya dara Naira tiriliyan N29.37 da aka samu a zango na uku na shekarar 2017.
Wani sashi na rahoton ya ce, "Tattalin arzikin kasar ya karu da 1.8% a zango na uku na shekarar 2018.
"Idan aka kwatanta da zango na uku na shekarar 2017 a lokacin da tattalin arzikin ya karu da 1.8%, an samu kari na 0.64% kenan.
"A zango na biyu na shekarar 2018 an samu habbakar tattalin arziki da 1.50% wanda ke nuna an samu kari na 0.31."
Wannan na nuna cewa an samu karuwar kudade a hannun al'umma da 'yan kasuwa da suke gudanar da hada-hadar yau da kullum.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng