An Shiga Tashin Hankali a Arewa, 'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutane 30 a Sabon Hari
- An shiga tashin hankali a wasu garuruwan jihar Benuwai yayin da 'yan ta'adda suka kashe mutane akalla 30 a jerin hare-hare
- An ce 'yan ta'addar sun ci karensu ba babbaka a garuruwan bayan sun ci karfin jami'an tsaro kafin jiragen yaki su fatattake su
- Shugabannin yankin sun roki gwamnati ta shiga lamarin, suna masu nuna girman asarar rayuka da dukiya da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benuwai - Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Katsina-Ala da Logo na jihar Benue.
Hare-haren sun fara a safiyar Lahadi, 24 ga Nuwamba, 2024, inda wasu 'yan bindiga suka mamaye kauyukan, aka jefa fargaba a zukatan jama'a.
An kashe mutane 30 a Benuwai
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a karamar hukumar Katsina-Ala, an gano gawarwaki 10, yayin da aka ce 'yan ta'addar sun cinnawa gidaje wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zuwa safiyar Litinin, 25 ga Nuwamba, hare-haren sun bazu zuwa karamar hukumar Logo, inda aka gano karin gawarwaki 20 bayan hare haren sun lafa.
Mazauna garuruwan sun nuna matukar damuwa kan irin arasar rayuka da dukiyoyin da suka yi, inda aka ce 'yan ta'addar sun kwashe kayayyakin jama'a da kona gidaje.
Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda
Daya daga cikin garuruwan da harin ya fi shafa shi ne Azege da ke karamar hukumar Logo, inda shaidu suka bayyana cewa 'yan ta'addar na amfani da makamai na zamani.
Cif Joseph Anawah ya bayyana cewa 'yan bindigar da suka kai farmaki garuruwan sun haura 300 kuma ana kyautata zaton bakin haure ne.
'Yan ta'addan sun yi amfani da mugayen makamai, lamarin da ya tilastawa mazauna garuruwan barin gidajensu, a cewar Cif Joseph.
Sai dai rahoto ya ce 'yan ta'addar sun ranta a na kare bayan da jiragen sojojin saman Najeriya suka fara luguden wuta a kansu.
Cif Joseph ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin bincike domin gano mutanen da suka bace yayin wannan tashin hankali.
Abin da ya jawo hare haren Benuwai
Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku, ya tabbatar da hare-haren da aka kai garin Adabo da Tse Gwebe a safiyar ranar Litinin.
Ya ce hare-haren sun faru da misalin karfe 2:00 na safe, inda 'yan ta'adda suka kashe mutane da kona gidaje.
Shugaban karamar hukumar Logo, Clement Kav, ya ce 'yan ta'addan sun yi ikirarin cewa su ne masu garin Tombo, kuma dole a bar masu garinsu, lamarin da ya jawo rikicin tun asali.
A cewarsa, 'yan ta'addan sun kashe mutum 17 a Tombo, kuma sun raunata kimanin mutane 37 kafin su bar yankin.
Mista Kav ya bayyana cewa gwamna ya tura jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren da abin ya shafa.
Hukumomi sun bayyana cewa halin tsaro a Benue yana kara muni, suna rokon gwamnati ta dauki matakin gaggawa.
'Yan bindiga sun kashe mutum 30 a Benuwai
A wani labarin makamancin wannan, mun rahoto cewa 'yan bindiga sun kashe akalla mutane 30 a kauyen Ayati, ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai.
Mazauna yankin sun bayyana cewa da yiwuwar waɗanda aka kashe a harin su haura 50 saboda har zuwa lokacin ana kan binciken gawarwaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng