Jihohin Arewa 5 da Suka Yi Fice Wurin Samar da Harajin VAT Mai Yawa a Najeriya
- Jihohi da dama a Najeriya sun samar da biliyoyi kudi na harajin VAT a cikin watan Agustan 2024
- Jihar Lagos ita ke kan gaba inda ta samar da akalla N249bn yayin da Rivers ke biye mata da N70bn
- Kano ita ta fi kowace jiha a Arewacin Najeriya samar da harajin (N4.65bn) sai Borno da ke biye da N3bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar tattara haraji a Najeriya (FIRS) ta fitar da wata sanarwa kan jihohin da suka samar da harajin VAT.
Hukumar ta ce jihar Lagos kadai ta samar da harajin fiye da jihohi 35 da suka samu a watan Agustan 2024.
Jihohin da suka samar da harajin VAT
Wani rahoto da TheCable ta fitar ya nuna yadda jihohi 36 da birnin Abuja suka samar da biliyoyi na harajin VAT.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai mafi yawan jihohin da suka fi samar da harajin sun fito ne daga yankin Kudancin kasar.
A wannan rahoto, Legit Hausa ta duba muku jihohin Arewa biyar da Abuja da suka fi samar da harajin a Najeriya a watan Agustan 2024.
1. Birnin Tarayya Abuja - N18.17bn
Babban birnin Tarayya da ke Abuja ita ce ta hudu a Najeriya da ta fi samar da harajin VAT a watan Agustan 2024.
Abuja da ke Tsakiyar Najeriya ta samar da akalla N18.17bn duba da cewa ita ce babban birnin kasar da ake hada-hadar kasuwanci da kuma kasancewar kamfanoni da ta ke haɗa al'ummar duniya gaba daya.
2. Jihar Kano - N4.65bn
Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ita ce ta shida a cikin jerin jihohi a fadin kasar baki daya game da harajin VAT.
Kano da ake yi wa lakabi da cibiyar kasuwanci ita ce jiha ta farko a Arewa da ta samar da harajin VAT mafi yawa.
Jihar ta samar da N4.65bn a watan Agustan 2024 duba da hada-hadar kasuwanci da ake yi da kuma yawan kamfanoni da ke jihar.
3. Jihar Borno - N3bn
Duk da matsalolin tsaro da jihar ke fama da su, Borno ta yi kokarin zama jiha ta biyu a Arewa game da samar da harajin VAT.
Jihar da ke Arewa maso Gabas duk da kalubalen da take fuskanta ta yi kaurin suna tun a baya wurin bunƙasar kasuwanci.
Borno ta samar da akalla N3bn wanda ya mayar da ita jiha ta 12 cikin jerin sauran jihohin game da harajin VAT.
4. Jihar Kwara - N2.89bn
Jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya ta samar da harajin VAT har N2.89bn a watan Agusta, Tribune ta ruwaito.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya yi namijin kokari wurin tabbatar da samar da yanayi mai kyau ga yan kasuwa da masu zuba hannun jari a jihar.
5. Jihar Adamawa - N2.59bn
Adamawa da ke Arewa maso Gabas ita ce ta biyu a yankin da ta samar da harajin VAT mafi yawa a cewar rahoton BusinessDay.
Jihar ta samar da N2.59bn na harajin wanda yana daga cikin hada-hadar kasuwanci da ke gudana a jihar.
6. Jihar Plateau - N2.58
Babban birnin jihar Plateau da ake kira Jos ya habaka wurin gudanar da kasuwanci da ke da tasiri a bangaren haraji.
Plateau ta kasance da yanayi mai kyau wanda mutane daga ciki da wajen kasar ke zuwa yawon bude ido da hakan ya kara inganta samar da kudin shiga da haraji mai yawa.
Gwamnatin Tinubu za ta kara harajin VAT
A baya, kun ji cewa bayan ta sha musanta cewa za ta kara VAT, gwamnatin Najeriya ta ce shirin gwamnati na kara harajin ya yi nisa.
Ministan kudi da tattalin arziki na kasa ne ya bayyana haka a taron masu zuba hannun jari da ya gudana a Washignton DC.
Mista Wale Edun ya ce majalisar tarayya na duba batun karin harajin, kuma ana sa ran kayan alatu za a yi wa sabon karin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng