Jihohi 4 da Yan Kwadago za Su iya Rufewa Saboda Gaza Ƙarin Albashi

Jihohi 4 da Yan Kwadago za Su iya Rufewa Saboda Gaza Ƙarin Albashi

  • Alamu sun nuna cewa za a iya samun matsala a wasu jihohi hudu da yan kwadago saboda zancen karin sabon mafi ƙarancin albashi
  • Kungiyar kwadago ta sanya ranar 1 ga watan Disamba a matsayin wa'adin da dukkan jihohi za su fara biyan mafi ƙarancin albashi
  • Yayin da wa'adin yan kungiyar kwadago ke kara matsowa, akwai jihohin Najeriya da ba su fara biyan mafi ƙarancin albashi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan kwadago na cigaba da saka ido ga jihohin Najeriya da ba su fara biyan mafi ƙarancin albashin ma'aikata ba.

Ma'aikata sun fara shiga yajin aikin gargadi a jihar Cross River saboda gaza samun sabon mafi ƙarancin albashi.

Kwadago
Jihohi 4 da ba a yanke matsaya kan karin albashi ba. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Jaridar the Nation ta yi rahoto a kan jihohi 4 da za a iya samun takaddama tsakanin gwamnoni da yan kungiyar kwadago.

Kara karanta wannan

Jigawa: Ma'aikata za su tsunduma yajin aiki kan rashin biyan sabon albashin N70000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohi 4 da NLC za ta iya rufewa

Yan kwadago sun sanya ranar 1 ga Disamba a matsayin wa'adin da jihohi za su ayyana sabon mafi ƙarancin albashi.

Sai dai yayin da ake kasa da mako daya ga cimma wa'adin, akwai alamun samun sabani da yan kwadago da zai iya kaiwa ga rufe jihohin:

  • Imo
  • Zamfara
  • Katsina
  • Cross River

Fara yajin aiki a jihar Cross River

A yayin da ake jiran fara cikar wa'adin yan kwadago, ma'aikata sun fara yajin aiki a jihar Cross River.

Ma'aikatan Cross River za su yi yajin aikin kwanaki biyu domin gargaɗin gwamnan jihar ya fara biyan mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan jihar ya yi kira ga yan kwadago da su yanje yajin aikin domin yana ƙoƙarin fara biyansu sabon mafi ƙarancin albashi.

NLC za ta rufe jihohi a Najeriya

Business Day ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta jaddada cewa duk jihar da ba ta fara biyan mafi ƙarancin albashi ba zuwa 1 ga Disamba za su tafi yajin aiki.

Kara karanta wannan

"Ba gudu ba ja da baya," NLC ta gargaɗi gwamnoni kan sabon mafi ƙarancin albashi

Yan kwadago sun ce abin da zai hana su tafiya yajin aiki kwai shi ne idan akwai alkawarin da aka yi da jiha a kan karin albashi.

Za a yi karin albashi a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma'aikatan gwamnati.

Mai Mala Buni ya amince da mafi ƙarancin albashi na N70,000 wanda za a fara biyan ma'aikatan gwamnatin jihar daga watan Disamban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng