Basussukan da Shugaba Bola Tinubu Ya Karbowa Najeriya a Shekarar 2024

Basussukan da Shugaba Bola Tinubu Ya Karbowa Najeriya a Shekarar 2024

A shekarar 2024 da ake bankwana da ita, gwamnatin Najeriya, a karkashin Bola Ahmed Tinubu ta karbo basussuka da su ka fusata wasu daga cikin 'yan kasar nan, musamman masana tattalin arziki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbo rancen kudade daga Bankin Duniya da sunan gudanar da ayyukan cigaban kasa da al'umar cikinta ta fuskoki da dama.

Tinubu
Masana sun shiga damuwa kan yawan bashin da Najeriya ke karbowa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin basussukan da gwamnatin Najeriya ta nema a shekarar nan ta cikin wannan rahoto;

1. Tinubu ya karbo basussuka daga Bankin Duniya

Jaridar Punch ta wallafa cewa, a cikin watanni 16, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta karbo rancen $6.45bn daga Bankin Duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta karbo basussukan da sunan gudanar da ayyuka daban-daban a bangarorin da su ka hada da;

Kara karanta wannan

TCN ta fadi biliyoyin da gwamnatin Tinubu ta kashe a gyaran turakun wuta 128

1. Dala miliyan $750 don ci gaban bangaren wutar lantarki.

2. Dala miliyan $500 don taimakawa mata.

3. Dala miliyan $700 don inganta ilimin 'ya 'ya mata matasa.

4. Dala miliyan $750 don samar da makamashi mai inganci ga muhalli.

5.Dala biliyan $1.5 don inganta tattalin arziki.

6. Dala miliyan $750 don gyara dabarun tara kudaden shiga.

2. Tinubu ya karbo bashin Dala Miliyan $500

Gwamnati ta karbo bashin daga Bankin Duniya wadata masu amfani da wutar lantarki da mtar wuta. Majalisar Dattawa ta amince da wannan bashi a watan Yuni 2024.

3. Tinubu na neman bashin Dala 2.2bn

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a kwanan nan, majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu na ranto $2.2bn don cike gibin ₦9.1 tiriliyan a kasafin kudin shekarar 2025.

Har yanzu ana tataburza kan lamarin, inda majalisar wakilai ta ke jan kafa bayan majalisar dattawa ta sahalewa shugaban ya karbo sabon gagarumin rancen.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara tuhumar Tinubu saboda batun karbo aron Naira Tiriliyan 1.7

Bashin Tinubu a nahangar tattalin arziki

Dr. AbdulNaseer Turawa Yola, malami ne a jami'ar Northwest da ke Kano, ya bayyanawa Legit cewa, ta fuskar tattalin arziki, cin bashi domin a gina kasa, ba laifi ba ne.

Masanin tattalin arzikin ya kara da cewa;

"A bayyane ya ke, kasashe da yawa sun ci bashi kuma sun gina tattalin arzikinsu.Amma inda ya ke zama laifi, shi ne in har kamar aka ci bashin amma ba a sa shi a doron gina tattalin arziki ba, ko aka ci bashin ya yi yawa."
Gwamnatin Najeriya kan tafka kuskure wajen karbo bashin da ba a sa shi a wajen gina tattalin arziki.

Ya kara da cewa amfani da kudin wajen sayo jiragen shugaban kasa da motoci ga 'yan majalisa na daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a karbo bashi.

Tinubu: Illolin karbo bashi ga Najeriya

Kara karanta wannan

Mai neman takara a PDP ya fallasa yadda aka rika biyan $30, 000 a saye tikitin 2023

Dr. AbdulNaseer Turawa Yola ya ce gwamnati kan yi amfani da kusan 30%-40% na kasafin kudin Najeriya wajen biyan basussukan da ta karbo da kudin ruwan da ke kai.

Dr. AbdulNaseer Turawa Yola ya ce;

""Wannan ba karamin illa ba ne, domin ya na nufin in babu wannan bashin, wannan kudi za a yi amfani da su ne wajen gina harkar ilimi, lafiya, masana'antu, sufuri da sauransu, wanda hakan kan kawo cigaban tattalin arziki."

Masanin ya kara da cewa abin tsoron a halin da ake ciki, shi ne yadda Najeriya ke cigaba da karbo sababbin basussuka, wanda za a gadarwa al'umma ta gaba.

Majalisa ta tuhumi Tinubu kan neman sabon bashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai sun bayyana takaicin yadda gwamnatin Najeriya ke neman sabon bashi duk da samun wasu kudaden.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ta samu adana akalla, $20bn daga cire tallafin man fetur, wanda ya sa wasu ke neman inda hukumomi su ka ajiye rarar kudaden.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.