Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Martani ga Kalaman Malamin Addini kan Sukar Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Martani ga Kalaman Malamin Addini kan Sukar Tinubu

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta musanta cewa shugaban kasa ya na daga cikin shugabannin Najeriya da suka samu mulki bisa kuskure
  • Malamin addinin kirista, Rabaran Mathew Kuka ne ya sanya Tinubu a cikin shugabannin da ba su da shiri su ka fara mulki
  • A martaninsa, hadimin Tinubu, Bayo Onanuga ya ce da shirinsa shugaban kasa ya kama mulkin Najeriya domin samar da cigaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaGwamnatin tarayya ya caccaki kalaman jagoran cocin katolika na jihar Sakkwato, Rabaran Mathew Kukah.

A ranar Lahadi ne malamin addinin ya bayyana Mai girma Bola Tinubu a cikin shugabannin da su ka samu mulki bisa kuskure.

Tinubu
Gwamnati ta ce Tinubu ya shirya mulkin Najeriya Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

A tattaunawarsa da jaridar Vanguard, hadimin Tinubu kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya yi kakkausan martani ga Rabaran Kuka.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa manufofin Tinubu suka kawo wahala da tsadar rayuwa a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Bola Tinubu ya shirya mulkin Najeriya,’ Onanuga

Jaridar Punch ta wallafa cewa Bayo Onanuga ya ce shugaban kasa, Bola Tinubu bai samu mulki bisa kuskure ba kamar yadda Mathew Kuka ya bayyana.

Ya bayyana cewa da shirinsa Bola Tinubu ya nemi mulkin kasar nan, kuma ya na daga cikin shugabannin da ke manufa wajen cigaban kasa da saukaka wahalhalu.

An fadi abin da Tinubu ke yi kan Najeriya

Hadimin Bola Ahmed Tinubu ya ce shugaban ya na bakin kokarinsa wajen magance matsalolin da su ka addabi yan kasar nan.

Bayo Onanuga ya kara da cewa;

“Ya na aiwatar da tsare-tsare, kuma ya san hakan zai shafi jama’a, saboda haka ya ke yin iya bakin kokarinsa wajen tallafawa jama’a domin a gudu tare a tsira tare.”

Dattawan Arewa sun gargadi Tinubu

A wani labarin kun ji cewa dattawan Arewacin Najeriya sun yi fatali da sabon kudurin harajin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi saboda illar da zai haifar ga yankin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan Arewa da suka nuna adawa da kudirin harajin Tinubu

Shugaban NEF, Farfesa Ango Abdullahi ya shawarci yan Arewa da su nuna adawarsu ga kudurin, ya yi zargin cewa ba a samar da shi da kyakkyawar manufa ga cigaban shiyyar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.