Gwamnatin Kebbi da Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara kan 'Yan Ta'addan Lakura

Gwamnatin Kebbi da Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara kan 'Yan Ta'addan Lakura

  • Ƴan ta'addan Lakurawa sun gamu da cikas a yunƙurin da suka yi na satar kayan mutane a jihar Kebbi a yankin Arewa maso Yamma
  • Gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunƙurin ƴan ta'addan su na satar shanu a wasu ƙauyuka
  • An samu nasarar daƙile mugun nufin ne dai na ƴan ta'addan bayan samun bayanan sirri kan shirinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi tare da goyon bayan jami’an tsaro sun samu nasara kan ƴan ta'addan Lakurawa.

Gwamnatin da jami'an tsaron sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin satar shanu da ƴan Lakurawa suka yi a ƙauyen Gamuzza, da ke ƙaramar hukumar Arewa da kuma ƙauyen Gwado da ke Bunza.

An dakile harin 'yan Lakurawa a Kebbi
Jami'an tsaro sun dakile yunkurin satar shanu na 'yan Lakurawa a Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami'an tsaro sun daƙile harin ƴan Lakurawa

Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartaswar jihar, AbdurRahnan Usman Zagga ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a wani hari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa martanin da aka mayar cikin gaggawa ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri game da ayyukan ƴan ta'addan.

Daraktan ya bayyana cewa bisa umarnin Gwamna Nasir Idris, rundunar sojojin saman Najeriya, da sojojin ƙasa sun garzaya wajen domin bibiyar gungun masu aikata laifukan.

Wane ƙoƙari gwamnan Kebbi ke yi kan tsaro?

AbdurRahman Zagga ya bayyana cewa Gwamna Nasir Idris a jajirce yake wajen kawar da ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa gwamnan a shirye yake wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Kebbi.

"Domin bunƙasa ayyukan tsaro, gwamna ya ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki da suka haɗa sarakunan gargajiya da jami'an tsaro ta hanyar yin tarurruka a kai a kai domin inganta musayar bayanai da haɗin kai."

- AbdurRahman Usman Zagga

An fatattaki ƴan ta'addan Lakurawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce jama'a sun fara ganin ayyukan dakarun sojojin kasar nan wajen korar yan ta'addan Lakurawa daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta nuna damuwa kan Boko Haram, ta ba sojoji umarni

Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubajar ne ya bayyana hakan bayan kai ziyarar aiki tare da duba kayayyakin yaƙin jirage na rundunar Operation Fansan Yamma, a jihar Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng